A Nijar Matasa na ci gaba da goyon bayan Sojojin CNSP
Shekaru uku bayan juyin mulki, yawancin majalisun matasa na masu ra’ayin cewa duk da matsalolin dake akwai, Sojoji na nasu kokari.
Wadannan matasan, yawancinsu tun farko sun goyi bayan juyin mulkin na Sojoji, a cikin majalisun matasa ana ci gaba da tafka muhawara, ga matashiya Fadila yanayin a yanzu ya canja lura da shekaru biyu baya.
« Gaskiya da farko mun dan ji tsoro, saboda ana cewa shi juyin mulki bai taba zama alheri ga kasa ba. A wani lokaci rayuwa akwai tsananin wahala, albashi bai zuwa kan lokaci, abinci ya yi tsada, abin dais ai godiya, amma yanzu Alhamdulillahi abubuwa na kyautatuwa»
Matasa a sahun gaba
A ra’ayin Abdurahaman, dole ne a jinjinawa Sojoji masu juyin mulki, wadanda suka saka matasa a cikin tafiyar al’amuran Kasa.
« A can baya lokacin siyasa na mulkin farar hula an mayar da matasa Saniyar ware a cikin wuraren daukar duk wasu muhimman shawarwari na ci gaban kasa, amma a yanzu hatta da Majalisar tuntuba da Kasa an saka matasa, wannan na nuni da cewa an fara saka matasan cikin tafiyar al’amura.
« abin da muka gani ma bayan juyin mulkin shine shugaban majalisar Matasa ta Kasa da shima matashi ne an nadashi a mukamin Minista, garemu wannan babban ci gaba ne da saka matasa cikin tafiyar aikin Kasa»
Matsalolin da za’a shawo kansu
Juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 ya kasance wani tushe na sake kwato yancin kasa, Ga Maman Sani, duk da cewa koyarwar da ake ma al’umma akan cimma wannan manufa ne, akwai kalubale da dama a gaba.
« abin babu sauki, akwai matsaloli musaman fannin shigar kudade a asusun gwamnati, akwai matsalar rashin aikin yi ga fannin rashin tsaro, harakokin jin dadin al’umma sannan da na ilimi a duk wadannan fannonin ana bukatar samun nasara don kaiwa ga ainafin cikakken yanci»
Albarkacin cikon shekaru uku da juyin mulkin Sojoji 26 ga watan Yuli ta zama rana ce ta Yanci da kishin kasa, gwamnati ta bukaci yan Nijar na kowane addini su gudanar da addu’o’i ga Kasa.

