Wasaf tsarin boyewa : abubuwan da zaku yi akan wannan manhaja ba tare da kun bar sawu ba

Wasaf tsarin boyewa : abubuwan da zaku yi akan wannan manhaja ba tare da kun bar sawu ba

Kare kiraye kirayenku, Dandalin da kuke ciki sannan da wasu sirrinku a Wasaf

Cikin Kuskure wani lokaci ku kan yada wani labari ga abokanku na Wasaf ba tare da ma kun sani ba. Musaman a loakcin da ku ke aiki da yanar Gizo, akwai hanyoyin da zaku bi don dakile duk wata sumbulewar wani abin da ba ku so wani ya gani cikin sauki da badda sawu ba cikin kwanciyar hankali.

Cikin Kuskure wani lokaci ku kan yada wani labari ga abokanku na Wasaf ba tare da ma kun sani ba. Musaman a loakcin da ku ke aiki da yanar Gizo, akwai hanyoyin da zaku bi don dakile duk wata sumbulewar wani abin da ba ku so wani ya gani cikin sauki da badda sawu ba cikin kwanciyar hankali.

Duk da cewa akwai tsarin badda kama, Manhajar Meta na aikewa abokanku wasu labarai naku kamar in kun karanta sako, da lokacin da suka sabka daga yanar Gizo, ko nuna foton da suka sa akan shafinku, domin samun natsuwa  Manhajar da bada damar saita duk wadannan abubuwan a cikin kankanen lokai.

Yadda zaku gyara tsarin kasancewarku kan layi ko kun karanta sako

Da farko zaku je a shafin saita abubuwa ko  Paramètres na Wasaf musaman bisa babbar waya ko Android sai ku shiga tagar Menu kuje inda aka rubuta Sirri ko Confidentialité. Daga nan wani sako zai zo muku na yin zabin abin da ku ke bukata, wani lokaci yakan bayyana a matsayin wata kalma ta ku fara tabtabcewa ko

 « Commencer la vérification » za a nuna muku tagogi guda hudu, wadda kuke shawa daga ciki shi zaku zaba wanda ake cema ku sa ido akan labaranku « Contrôler vos informations personnelles », sauran tagogin ma suna iya taimaka muku. Ko ku bi wannan hanyar ko kuma wasu hanyoyin da tsarin Wasaf ya tanada duk dai wuri daya ne abin zai kai ku.

Sai ku shiga dandalin naku musaman inda ku ke dora foto « Photo de profil » kuna iya zabar wanda zai ganin foton naku, kowa ne zai gani, ko wadanda ke cikin wayarku kadai, ko ku zabi wadanda ku ke son su gani banda wasu, ko kuwa bak u son kowa ma y aga foton naku.

Abu mai amfani sosaia, ganinku a kan layi  « Présence en ligne » akwai inda za a ganin lokacin da kuke akan yanar Gizo wannan kuma baida amfani ga mai son rayuwar sirri, don haka akwai wurin da zaku iya kashe wannan ya zama sam ba a ganinku ko na wani dan lokaci  idan kun hau yanar Gizo, ko ku zabi wadanda zasu ganinku sauran ku zuba su a shara. Sai dai wani hamzari ba gudu ba, idan kuka rufe ba a ganinku a yanar Gizo haka kuma ba zaku ga wasu daga abokan huldarku ba. Duka dai a cikin tagar kasancewa a layin yanar Gizo  « Présence en ligne », kuna iya sanar da abokan huldarku kai tsaye in kun hau yanar Gizo ta Wasaf.

Wani abu mai matukar muhimmanci shine tsarin ganin in ka karanta sako: Confirmations de lecture. Idan kuka rufe wannan tagar abokan huldarku ba zasu ganin in kun karanta sakonninsu na murya ko na rubutu ba, don haka sai ku soke tagar da launin toka toka abin da zai hanasu daukar launin bula dake nuna kun karanta. Hakanan kuma ba zaku ganin abokan huldarku idan sun karanta sakoninku ba. Sai daia cikin tattaunawar Dandali ko Groupe bak u iya dakatar da wadannan abubuwana da muka zana a sama.zaku iya yin wannan ne a shafinku na ku kadai.

Idan kuma kuna son karanta wani sakon murya ba tare da an gano kun karanta ba akwai hanya, sai ku aikawa kanku sakon a wani wurin aje murya da kuka riga kuka yiwa kanku, zaku iya sauraren muryar idan kuka danne abin da ya aiko ku saurara ba tare da ya gano kun saurara ba.

Kare kiraye kirayenku, Dandalin da kuke ciki sannan da wasu sirrinku a Wasaf

Wadannan tagogi sune zaku wa gyaran fuska don tsare sirrinku a daina ganinku akan manhajar Wasaf.

Da farko zaku shiga a babbar taga cewa da Confidentialité, zaku iya zabar wadanda zasu ganin abin da zaku wallafa, akwai tsarin da zaku iya sakawa na yawan sakonnin da z a aiya gani don kada ku a san kun kasance a yanar Gizo, zaku zabi wadanda zasu kiraku, sannan kuna iya saka tsarin kiran da ba aji ko silencieux idan bak u san wanda ya kiraku ba ko Inconnu. Wannan zai tsare muku tushen gano lambarku ko IP lokacin da ku ke kira  sai ku shiga tagar Paramètres avancés du menu Confidentialité. A karshe don batar da kama a bar samun lambarku cikin sauki, kuna iya zaben wani suna na daban akan dandalinku ko Profil da za adinga tuntubarku a kansa maimakon lambar wayarku

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )