Yadda malaman makaranta  ke gudanar da sana’o’i domin cike gibin rayuwa lokacin babban hutu.

Yadda malaman makaranta  ke gudanar da sana’o’i domin cike gibin rayuwa lokacin babban hutu.

A lokacin hutun makaranta, malamai da dama suna amfani da wannan lokacin wajen gudanar da sana'o'i domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga

Wasu Malaman sun karkata zuwa kasuwanci a Maradi lokacin hutu musaman diya Mata

Hutun makaranta dake daukar watanni uku,  galibi lokaci ne na hutu da shakatawa. Amma ga malamai da dama, wannan lokaci ba na zama babu aiki ba ne. Saboda matsalolin tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa, da yawa daga cikinsu na shiga wasu ayyukan yi domin ƙara samun kuɗin shiga. Tukin Adaidaita Sahu, kasuwanci ko kuma koyar da darussan a gidaje don dalibai masu rauni,  waɗannan malamai na amfani da lokacinsu na hutu maimakon zaman kashe wando da hirarrakin banza.

Shamsudine Hamza malamin makarantar sakandare ne a Maradi wanda ke  amfani da hutunsa wajen yin wani aiki na daban. Yana tuka babur mai ƙafa uku domin ƙara samun kuɗin shiga da kuma kula da bukatun iyalinsa. Yana mai cewa.

« Muna da lokaci mai yawa a lokacin hutu. Maimakon mu zauna ba tare da yin komai ba, duk da binciken da muke yi da kuma horaswar da muke samu, muna ƙoƙarin nemo wasu ayyuka banda koyarwa. A yau ni direban Adaidaita Sahu ne. Alhamdulillahi, wannan aikin yana taimaka mini wajen biyan wasu daga cikin bukatuna, har ma ina iya taimaka wa wasu mutane. »

Wasu Malaman sun karkata zuwa kasuwanci a Maradi lokacin hutu musaman diya Mata.

Rayanatou, wadda ke cikin shekaru ashirin da haihuwa, ita ma malamar makaranta ce kuma tana yin kasuwanci ta yanar Gizo. Bayan ta shafe lokaci tana sawo kayayyaki daga Najeriya, yanzu tana sayen kayayyakin ne a Maradi. Wannan sana’a tana ba ta damar samun ƙarin kuɗin shiga. Inji ta

« Da yake yanzu muna hutun makaranta, ina yin kasuwancina ne  ta intanet. A da ina siyen kayayyaki daga Najeriya ina kawo su ina sayarwa, kuma hakan yana ba ni riba. Amma saboda matsalar rashin tsaro a kan hanya, na daina zuwa Najeriya domin sayen kayayyaki. »

Yanzu Rayanatou ta ce tana sayen kayayyaki ne a kasuwar Sonitan da ke Maradi domin rage kuɗin sufuri da kuma ƙara ribarta, ko da kuwa ribar ba ta da yawa.a cewarta

« Ina siyen kayayyaki a kasuwar Sonitan,  sannan ina sake sayar da su. Ko da ribar ba ta da yawa, aƙalla ina samun wani abu. »

Wasu kuma sun ci gaba da aiki a fannin ilimi.

A nasa ɓangaren, Saminou Adamou Abass yana amfani da hutun makaranta wajen koyar da darussan ƙarin bayani ga ɗaliban aji uku na kwaleji masu rauni kafin komawa karatun sabuwar shekara. Wannan mataki yana ba shi damar ci gaba da aikinsa na koyarwa tare da samun ƙarin kuɗin shiga. Ga  abin da yake cewa.

« Domin kada mu zauna a gida hannu biyu, mun fara shirya darussan ƙarin bayani a lokacin hutu. Muna koyar da ɗaliban da za su rubuta jarabawa. Kuɗin da muke karɓa kaɗan ne, kowane ɗalibi yana biyan CFA jika  biyu kacal. Ba wai don samun kuɗi mai yawa ba ne, sai dai don kada mu yi aikin kyauta. Muna gudanar da waɗannan darussan a makarantar Mufida Faramare. »

A lokacin hutun makaranta, malamai da dama suna amfani da wannan lokacin wajen gudanar da sana’o’i domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga. Wannan na nuna da irin ƙalubalen tattalin arziki da gidaje da dama ke fuskanta. Sai dai kuma akwai wasu da ke amfani da hutunsu wajen aikin sa-kai a wasu kungiyoyi ko ayyukan ci gaban al’umma domin bayar da tasu gudummawa ga ci gaban yankinsu.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )