
Mai horas da kungiyar Mena ta Nijar. Badu Ezaki ya yi murabus
muna baiwa yan kasa tabbacin cewa, zamu samo hanyar magance wannan matsalar da ci gaba da aikin akan abin da ya yi, saboda ba zamu cewa mu sake komai tun daga farko ba, zamu dasa inda ya bari kuma zamu samo mafita
Kwallon kafa : mai horas da kungiyar Mena ta Nijar. Badu Ezaki ya yi murabus
Mai horas da MENA cewa da (kungiyar kwallon kafa ta kasa ) Badu Ezaki ya yi murabus daga mukaminsa, shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijar Isaka Adamu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya jagoranta ranar Lahadi a birnin Yamai.
A cewar shugabannin kwallon kafa na kasar Nijar, murabus din kwarraren dan kasar Moroko« Babban cikas ne a garesu», duk da cewa « Badu Zaki tun zuwansa ya yi matukar aiki da ya kawo ci gaba ga kungiyar ta kasa , da yan kwallon da ma magabatan kwallo na kusa da shi ».
Wannan matakin murabus da ya dauka na zuwa ne a wani lokaci da kasar Nijar ke shirye shiryen shiga tankade da rairaye don zuwa gasar cin kofin Afirka ta 2027 da kasashen Uganda, Kenya da Tanzaniya zasu shirya.
Kwallayen da Nijar zata buga zasu kasance a ranekun na jadawalin da hukumar kwallon Duniya Fifa ta tsara, ranekun 1 da 2 da kuma 21 ga Satumba sai 6 ga Oktoba na 2026 ; hakanan akwai zagaye na biyu a ranekun 3 da 4 da 9 zuwa 17 ga Nuwamban 2026 ; sai ranekun 5 da 6 sai 22 zuwa 30 ga watan Maris 2027.
« Muna da cikakken fatan samun nasara lura da wannan gagarumin aikin da ya gabatar ,amma duk da haka ( ya yi murabus ) saboda wasu dalilai na kashin kansa », Inji Isaka Adamu da yake magana akan mai horaswar. « Gaskiya abin ya bamu mamaki da jin wannan batu na murabus din nasa »,sai dai muna da kyaukyawan fata inji Isaka Adamu shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijar.
« abin da nike son mutane su rike , shine cewa wannan murabus din nasa bai da wani tasiri akan burin da muka sa gaba, munada kwarin guiwar cewa yanzu ne ma muke jin karfin cewa zamu samu damar zuwa gasar cin kofin Afirka mai zuwa », Isaka Adamu ya kara da cewa .
« Dalili shine yanzu muna cikin gina cikakkar kungiya ta kasa, ba wai mun dogara da mutum guda ba ne, a tare da wannan kungiya akwai lallai wani hadin kai da ci gaban da ya kawo, wadanda mun karu da su kuma zamu aiki da su.» inji shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijar, garesh tafiyar Dan kasar Morokon ba karshen Duniya ba ne.
« muna baiwa yan kasa tabbacin cewa, zamu samo hanyar magance wannan matsalar da ci gaba da aikin akan abin da ya yi, saboda ba zamu cewa mu sake komai tun daga farko ba, zamu dasa inda ya bari kuma zamu samo mafita », inji Isaka Adamu .
« Neman zuwa gasar cin kofin Afirka zai fara ne a watan Satumba mai zuwa don haka a yanzu muna jajibirin soma tankade da rairayen ne », Isaka Adamu ya jaddada wannan ne don zama « wani muhimmin sako ga yan kwallon da masu kula da su domin basu kwarin guiwa sannan da kira ga kowa ya kama ».
Game da batun canjin Badu Zaki shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijar ya ce sun samu tayi da dama daga masu horaswa.
« mun samu labarin murabus din Badu zaki ne ranar 19 ga watan Yuli, a yau muna 26 ga watan Yuli, ban iya fada muku yawan takardun bukatar da muka samu na masu horaswa dake son zuwa Nijar», inji Isala Adamu .

