Kamfanin SpaceX na shirin samar da wayar salula mai tafe da yanar gizo don kara karfin Starlink

Kamfanin SpaceX na shirin samar da wayar salula mai tafe da yanar gizo don kara karfin Starlink

Gagarimin tsari da burin kamfanin SpaceX don samar da wayar salula mai yanar gizo a ko’ina da zai yiwa sauran kamfanoni zarra su kasa yin gogayya da shi.

Kamfanin SpaceX na shirin kara karfin da armashin Starlink ta hanyar samar da wayar salula da zaka samu yanar gizo ko’ina ta hanyar tauraron Dan Adam, wannan kuma ta kara wasu kananan eriya ga tauraron Dan Adam da suke halbawa a sararin samaniya nan bada jimawa ba.

Bayan da wani sashen tauraron Dan Adam na Kamfanin SpaceX a yan kwanakin nan ya fada akan Duniyar wata, Kamfanin ’Elon Musk na shirin fadada sashensa na sadarwa zuwa wayar salula mai aiki kai tsaye da yanar Gizo ko Intanet, karawa  Starlink karfi a dinga yawo ko’ina  cikin aljihu da intanet mai karfi wata hanya ce ta rike masu amfani da kayansa, sannan da yin zarra ga sauran kamfanonin dake cikin wannan sashe na sadarwa irin wadda aka sani.

Gagarimin tsari da burin kamfanin SpaceX don samar da wayar salular da zai yiwa  sauran kamfanoni zarra su kasa yin gogayya da shi

Sakamakon saye hanyoyin sadarwa na kamfanin EchoStar bayan wani ciniki na dalar biliyon 17, Kamfanin  SpaceX na son dora sashensa na Starlink ga wasu kananan eriyoyi da zasu sa kananan wayoyi su dinga kama yanar Gizo mai karfi, abin da kamfanin ke kira Direct to Cell.

Yayin da take gabatar da rahoton shekara na kudaden kamfanin, shugabar kamfanin Space X  mai suna Gwynne Shotwell, ta sanar da wannan sabon tsarin da suke son fitarwa  don kara samun kudade musaman a shekara mai zuwa ta 2027 ta hanyar samar da karfin Megahetz 65 mégahertz . Tsarin na kafa eriyoyi a wurare daban daban irin na zamani zai sa kamfanin ba zai kashe kudade dayawa ba, ta hanyar eriyoyin da ake kira  femtocells da za a fada da wani kwagiri mai kamo maganadisun na yanar gizo kuma wannan zai magance matsalar samun yanar gizon cikin sauki da wasu lokutan manyan gidaje na kankare da cikin birane ke hanawa kaiwa yadda ake so.

Duk da cewa kaddamar da wannan sabon tsarin sai karshen shekara mai zuwa ata 2027, akwai ayoyin tambayoyin da ake azawa, musaman akan yadda kamfanin zai shawo kan magabata domin su amince da bashi damar amfani da wannan sabuwar hanyar ta musaman don samarwa al’umma yanar gizo mai karfi.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )