ILLAR WATSI DA TARBIYAR YARA MATASA DA IYAYE KE HAIFARWAR  CIKIN AL UMMA .

ILLAR WATSI DA TARBIYAR YARA MATASA DA IYAYE KE HAIFARWAR CIKIN AL UMMA .

«   musali yanzu yara basama dattizawa ladabi , allah cewa yayi masu imani ku kiyaye kanku da diyanku daga wuta.don haka addini yace a koya ma yaro ladabi in zaici abinci yace bissimilahi kuma yaci abincin gabanshi»

A yau, da dama daga cikin matsalolin da al’ummar Nijar ke fuskanta suna da nasaba da ta’addancin matasa, wanda a wasu lokuta ke haifar da mummunan tasiri ga tsaron al’umma, zaman lafiya da kuma makomar matasan ƙasar.Wannan matsala na da nasaba da yadda wasu iyaye suka yi watsi da nauyin da ke kansu na tarbiyyantar da ‘ya’yansu, lamarin da ke haifar da illoli masu yawa a cikin al’umma.

 

A cewar  Abdou Dan Malan, masanin zamantakewar al’umma a Maradi komi ya gurbace sabuda iyaye sunyi watsi da tarbiyar ya ’yansu «Yau in muka duba watsi da iyaye sukayi wajen tarbiyantar da diyansu yasa komi ya gurbace ,shaye shaye yayi yawa ga matasa,yara ba ladabi,mutane sun lalace ,ga ta’adanci sai karuwa yake cikin a’umma sata duk abubuwa na asha nata karuwa..kowa nada kokarin da zai iya badawa wajen tarbiyantar da yara amma uyaye tun cikin gida ya zama cilas su maida hankali wajen tarbiyar diyansu» .

Dukkanin addinai sun tanadi cewa iyaye sune keda cikakken alhakin kula da tarbiyya da kuma ɗaukar nauyin ‘ya’yansu .

Cheikh Abou Saley mai wa’azi  anan cikin jahar Maradi yayi  sharhi, kan cewa « Ita tarbiyar, na farko wanda allah ya dorama ita sune uwaye ,na biyu kasa bai kamata kasar wadda akwai musulmi cikin ta ba ace komi anayi.ita tarbiyar ilimi ne da aiki dashi ,sabani yadda wasu uwaye  sukayi ma tarbiya munmunar fahinta suke cewa sun kashe kudade da dama don tarbiyar ya’yansu. » a cewar sa. 

Cheikh Abou Saley yayi tir da Allah wadai  da rashin girmama latizawa da wasu yara ke yi «   musali yanzu yara basama dattizawa ladabi , allah cewa yayi masu imani ku kiyaye kanku da diyanku daga wuta.don haka addini yace a koya ma yaro ladabi in zaici abinci yace bissimilahi kuma yaci abincin gabanshi» .

A cikin ‘yan shekarun nan, ana samun ƙaruwa a aikata laifuka a birane, musamman yawaitar satar jaka ko waya da ƙarfi, fasa gidaje da kuma hare-haren da ake kaiwa da makamai, musamman a manyan biranen ƙasar. Wannan yanayi ya kuma taimaka wajen ƙaruwa da tashe-tashen hankula, inda a wasu lokuta har ake samun kisan gilla a cikin al’umma.

Ahadi Moussa.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )