kofin Afirka ta  2032 : Kasashen Nijar, Mali da  Burkina na takarar shirya gasar  tare

kofin Afirka ta  2032 : Kasashen Nijar, Mali da  Burkina na takarar shirya gasar  tare

. Matsalar rashin tsaro na iya zama wani babban kalubale ga kasashen na yankin Sahel ga shirya gasar Cin kofin Afirka a 2032

Hukumomin kwallon kafa na kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun bayyana aje takararsu ta hadin guiwar kasashe uku na AES don shirya gasar kofin Afirka ta 2032.  

Yayin da hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta bukaci kasashen nahiyar dake son shirya gasar a shekarun 2028, 2032 da 2036, su aje takardunsu, hukumomin kwallon kafa na kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun bayyana aje takararsu ta hadin guiwar kasashen uku don shirya gasar a 2032.  

A cikin hata sanarwar hadin guiwa hukumar kwallon kafa ta Nijar da takwararta ta Mali (FEMAFOOT) sun bayyana anniyar kasashe uku na AES na shirya ita wannan gasa tare da aje takardun bukatar hakan ga hukumar ta CAF a Birnin New York na Amurka ya yin wani taro da shugaban hukumar ta CAF dan kasar Afirka ta kudu  Patrice Motsepe ya jagoranta. A cewar shugaban hukumar wannan takarar ta kasashen AES su uku na da sa’ar ta samu karbuwa ga hukumar tasa, ga yanzu wannan takarar dai itace ta farko da wasu kasashen Afirkar suka nuna. Yanzu ya rage shirye shirya da cika ka’idojin da hukumar da shata kafin baiwa kasashen damar shirya wannan gasa, Kasashen Mali da Burkina faso da suka taba shirya wannan gasa na da filayen da za a iya buga wassani a kansu don haka wannan hadin guiwar nada matukar tasiri.  

Yanzu dai a hukumance kasashen uku na AES sun aje takararsu ta shirya gasar cin kofin Afirka ta 2032, a cikin wata sanarwa ta ranar Litinin 20 ga watan Yuli 2026 ne hukumar kwallon kafa ta Nijar (FENIFOOT) ta sanar cewa kasashen Burkina Faso, Mali da  Nijar na takarar hadin guiwa don shirya gasar cin kofin Afirka  (CAN) ta 2032.

Kamar yadda doka mai lamba  7.3 ta tsarin neman takara  na (CAF) ta shata, hukumomin kwallon kafa na kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun aje takardun neman takararsu ta shirya gasar cin kofin Afirka ta  CAN 2032.

Wannan ka’idar ta karbar takardar neman takarar shirya gasar da hukumar kwallon Afirka  CAF ta tilastawa kasashen su aje,  dama ce garesu na ci gaba cikin bin hayar kaiwa ga samun nasara .

A cewar wata majiya mai tushe daga hukumar kwallon kafa ta Nijar (FENIFOOT), a cikin wannan tafiya ta neman shirya gasar ta 2032, an yi wata ganawa a birnin New York na Amurka ranar 18 ga watan Yulin 2026 tsakanin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF), Dakta Patrice Motsepe, da shugabannin hukumomin kwallon kafa na Burkina Faso,  Mali da Nijar . « ya yin taron an canza yawu kuma hukumar CAF ta amince da karbar takardun neman takarar na kasashen AES  a 2032 », inji sanarwa

« Shugaban hukumar kwallon Afirka ta CAF [Patrice Motsepe,]  yace wannan niyya ta kasashen uku na AES don shurya gasar a 2032 abin yabawa ne, musaman ganin hadin guiwa abi ne na yarda da juna sannan da darrata juna sai dai fatansa shine ayi abin cikin ka’idodjin da hukumarsa ta CAF ta shimfida wajan neman takarar.» Inji sanarwar Hukumar kwallon Nijar Fenifoot

Kalubale da jiran da akewa wannan shiri na kasashen AES na neman shirya gasar cin kofin Afirka  da alama yake da haske

Hukumomin kwallon kafa na kasashen uku daga yanzu zasu yi aiki tare  don shirya wannan takarar yadda ya dace.

Yanzu ya ragewa kasashe uku na AES na su shirya takardun da zasu gamsar da hukuamr kwallon kafar ta CAF domin samun tikitin shirya gasar a 2032. Wannan kuma babban kalubale ne lura da yadda hukumar CAF ke tsaurarawa kafin baiwa kasa damar shirya gasar wace kasashen na AES zasu shirya nan da shekaru 6 masu zuwa.

Bisa takardai kasashen Burkina Faso da Mali ,a sahun gaba saboda a can baya sun taba shirya gasar, babban kalubale ga Nijar yace wace a yanzu bata da filin kwallon da ya cancanci karbar manyan wasanni irin na kasa da kasa. Matsalar rashin tsaro na iya zama wani babban kalubale ga kasashen na yankin Sahel , sai dai watakila ko wannan neman takarar zai sa kasashen su tashi tsaye haikan wajan samar da tsaron a yankunansu.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )