Mummunan hadari kusa da Madawa : a kalla mutane 21 ne suka rasu saka makon karo tsakanin motocin safa biyu
muhawara akan sha’anin kare rayukan al’umma masu balaguro akan hanyoyin Nijar, musaman muhimmancin darrata ka’idojin tuki da batun rage gudun motocin na safa ko bus
Mummunan hadarin hanyar ya hada motocin safa biyu daya ta kamfanin STM da wata ta Kamfanin SONITRAV ya faru ne a yau Juma’a 7 ga watan Agusta kusan shiga garin Madawa na Jihar Tawa, alkaluman wucin gadi na nuni da cewa hadarin ya lakume rayukan mutane 21 da wasu da su aji mumaman raunuka.

Samun labarin keda wuya gwamnan Jihar Tawa yak ai ziyara a wurin da lamarin ya faru don ganin da ido halin da ake ciki dangane da wannan bala’i da ya faru. Gwamnan ya nuna alhini da kaduwarsa akan abin da ya faru tare da bada umurnn gaggauta kai wadanda suka ji ciwo a asibitin Madawa domin daukar nauyinsu.
Rahotannin farko da aka samu a inda lamrin ya faru, na cewa
Gudun da ya wuce kima ne sababin wannan mummunan hadarin, hukumomi dai na ci gaba da gudanar da bincike don sanin ainafin abin da ya haddasa hadarin
Wannan sabon hadari ya kara jefa muhawara akan sha’anin kare rayukan al’umma masu balaguro akan hanyoyin Nijar, musaman muhimmancin darrata ka’idojin tuki da batun rage gudun motocin na safa ko bus, da wasu direbobin ba sa yi duk da cewa suna dauke da rayuwar jama’a da suke wasa da ita