
Bikin tuni da Ranar dashen itace na 2026 Dorowa don sake raya kasar noma
Dorowa icen da aka fifita a sallar itace ta bana 2026
Dorowa icen da aka fifita a sallar itace ta bana.
Ta hanyar dasa icensa ne dake cike da tarihi shugaban kasar Abdurahaman Cani ya kaddamar da bikin sallar itace ta bana 3 ga watan Agusta 2026. Icen Dorawa ne aka zaba a bana a matsayin icen da aka fifita wajan raya kasar noma sannan da kare muhalli.
Bayan dasa icen na shugaban kasa suma dimbin Matasan da suka halarci bikin kowa dauke da icensa na Dorawa da ya dasa don kawo tasa gudumawa wajan maido da itacenmu dake kan hanyar bacewa tare da raya kasa da yaki don maido da kasar noman da ta zaizaye.
Ga wadannan daruruwan Matasan dama ce ta bayar da tasu gudumawa wajan yaki da canji da dumamar yanayi inji Aussuk Islaman na kungiyar Matasan Nijar masu yaki da dumamar yanayi yana mai cewa. « Dama ce irin wannan rana na bayar da kokari da kara himma wajan shuka itace masu yawa don kare muhalli, A matsayinmu na matasa kuma yan Nijar ta irin wannan aikin ne na shuka itace ya kamata mu bada namu taimako don maido da kasar noman da ta zaizaye sannan da sake maido da itacenmu dake kan hanyar bacewa. »
Ramatu Musa, wata matashiyar yan gwagwarmayar kare muhalli ta bayar da shidar dalilan muhimmancin shuka itace « wannan ice na dorawa yanada matukar muhimmanci da amfani mai yawa, idan ya girma za mu amfani da yayansa muna yin lemo na sha, ga kunnuwansa dake matsayin cikakken taki don taimakawa gonakinmu haka da samar da abinci ga dabbobinmu.»
Dorowa ice mai amfani kala kala
Wannan gangami bai tsaya ga matasa kadai ba, dattijawa masu shekaru da yawa suma sun hallara a wannan biki don dasa itacen da yayansu da jikokinsu na gaba zasu amfana . Uwargida Amina Mutari, masahwarciya ce a Da’irar Dan Isa tana mai cewa « Na shuka wannan icen ne na san da ko ban ci yayansa ba ina raye, yaya da jikokina zasu amfana da inuwarsa, yayansa da ake sarrafa daddawa da su ».
Kira ga Matasa na su dauki nauyin da ya rataya a kansu
Wannan bikin dashen itace bai bar kowa baya ba, Mai Martaba Sultan na Damagaram Abubakar Sanda Umaru yace matasa ne ya dace su kare muhalli a yanzu.
A cewarsa , « Wajibi ne matasa su baiwa wannan lamari na dashen itace cikakken goyon baya, saboda sune nauyin ya rataya a kansu, tun da ance yara manyan gobe. Mu manya munyi iyakar namu kokari yanzu ya rage wa matasa su yi nasu ta hanyar kula da wadannan itacen da muka dasa saboda zuwa badi ace dukansu sun kama».
Kadada ko Eka 50 ne aka kewaye inda aka dasa itatuwa dubu 15
A jimilce itatuwan Dorowa dubu 15 ne aka aka shuka a wani wuri da aka kebe aka kewaye tare da samar da ruwa da tsaro don samun nasarar ci gaban wadannan itatuwa na Dorowa su girma har a ci moriyarsu. Zaben wannan ice na dorawa na da matukar muhimmanci saboda yana cikin itatuwanmu na gargajiya dake kan hanyar bacewa duk da amfaninsa kala kala ga bunkasa tattalin arzikin mutanen karkara da al’umma baki daya.
A cewar darakta Janar da ma’aikatar kare muhalli ta kasa Kanal Lawali Sumaila, « A yanzu siyasar kare gandun daji itace maido da itatuwanmu na gargajiya dake kan hanyar bacewa, wannan nada matukar muhimmanci ga mutanenmu na karkara dake zama kashi 80 na yawan al’umma».
Don baiwa yan baya gado na gari
Wadannan matasan ba wai suna dasa itatuwa ba ne kawai, sun dauki alkawarin kare muhalli da gandun daji tare da sake raya wuraren da suka zaizaye don jin dadinsu zuwa gaba

