Maradi: Mata na yawan kai ƙorafe-ƙorafen cin zarafi a gidajen aure wajen Alkali

A fadar Mai Martaba Sultan Ahmed Ali Zaki, gidan Alkali na daga cikin wuraren da al’umma ke kai ƙorafe-ƙorafe domin neman mafita ga matsalolin da suke fuskanta. Sai dai a wannan lokaci, mata ne ke yawan zuwa wajen Alkali domin neman mafita kan matsalolin da suka shafi zamantakewar aure da mazajensu.

 

Matsalolin da ake gabatarwa sun haɗa da rashin ciyarwa da kula da iyali, cin zarafi, duka da kuma zagi da wulaƙanci.

 

Rashin ciyarwa da kulawa

 

Barka, wata matashiyar mata mai shayar da ɗanta namiji, na daga cikin matan da suka tunkari gidan Alkali domin neman a sauƙaƙa mata zaman aure. Ta ce rashin samun sutura da kuma abinci ya sa ta kasa ci gaba da rayuwar da take ciki.

 

«“Kawai zaman ne ya ishe ni. Tunda suturar babu, abinci ma na dare ne; idan ya ba ni yau, sai wani dare. Shi ya sa yanzu bukatata kawai shi ne ya sake ni. Wannan shi ne dalilin zuwana nan.”»

 

Barka ta ce an taɓa shawo kanta ta koma gidan mijinta, amma har yanzu ba ta ga wani sauyi ba. Haka kuma ta bayyana cewa ɗanta, wanda yanzu ya kai shekara guda da watanni huɗu, bai samu isasshen kulawa daga wajen mahaifinsa ba.

 

Ta ce a baya wata ’yar uwa ce ke taimaka mata da jari domin ta riƙa sayar da turare, amma kuɗin sun ƙare, abin da ya ƙara tsananta mata halin rayuwa.

 

Zargi, zagi da tashin hankali

 

Irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe na yawan kaiwa wajen Alkali. Kando, wata uwa, ta bayyana cewa ta je wurin ne bayan ’yar’uwarta ta nemi taimakonta kan matsalar da take fuskanta a gidanta.

 

«“Tun ƙarfe uku na dare, ’yar magajina ta zo ta same ni. Ta ce min tsakaninta da mijinta babu mutunci, sai tashin hankali da wulaƙanci.”»

 

A cewar Kando, duk da cewa ’yar’uwarta ba ta rasa abinci ko abin sha, tana fuskantar zagi da kuma duka daga mijinta.

 

Ta ce a wani lokaci mijin ya yi amfani da fanka wajen dukanta, lamarin da ya jawo mata rauni a fuska har aka yi mata ɗinki.

 

Kando ta kuma ce matar na fuskantar zarge-zarge da kalaman batanci daga mijinta, ciki har da zargin tana neman wasu maza da kuma cin mutunci ga mahaifiyarta. A cewarta, wannan lamari ya yi matuƙar shafar mahaifiyar matar.

 

Alkali ya fi karkata ga sasanci

 

Alkali Lawali Mai Dala’ilu ya ce mata da dama ne ke zuwa gabansa domin gabatar da ƙorafe-ƙorafe da suka shafi rashin abinci da kuma cin zarafi a cikin gidajen aure.

 

Ya bayyana cewa idan iyaye suka ji ana tauye ’yarsu ko ana dukanta, yana da wahala su yi shiru ba tare da neman mafita ba.

 

A cewarsa, hanyar da ake fara bi ita ce sasanci tsakanin ma’auratan, tare da jan hankalin wanda ake zargi da cin zarafi da ya daina duka da sauran munanan halaye.

 

«“Alkali yana ƙoƙarin yin sasanci, tare da cewa mai bugun ko dukar mata ya bari. Idan bai bari ba, sai mu tura lamarin zuwa kotu ko ’yan sanda. Idan har hakan ma bai samu ba, dole mu kai lamarin inda ya dace, har ma da hukumomin da ke kula da yara, tare da yiwuwar kai shi ga UNICEF.”»

 

Yawaitar irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe a wajen Alkali na nuna irin matsalolin da wasu mata ke fuskanta a cikin gidajen aurensu. Matasa mata na daga cikin waɗanda ake yawan ji suna neman taimako domin samun mafita ga matsalolin zamantakewar aure, musamman waɗanda suka shafi kulawa, cin zarafi da tashin hankali.

Illia Moumouni

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )