A Maradi, mata yan kasuwa masu zuwa Nigeria na fuskantar kalubali bisa hanya

A Maradi, mata yan kasuwa masu zuwa Nigeria na fuskantar kalubali bisa hanya

Kasuwacin zuwa  Najeriya dai  na daya daga cikin hanyoyin da Mata da dama ke samun kudin shiga  anan Maradi. Kama daga zuwa Magama, Jibiya Katsina har kano da su Mashi su mai Aduwa, babu kasuwannin da Matan ba su ci, yawancinsu ko dai Mazajensu sun mutu sun bar musu Marayu

kasuwancin ƙetare da ake yi tsakanin Nijar da Najeriya na daga cikin muhimman hanyoyin samun kuɗin shiga ga mata da dama. Kullum, waɗannan mata kan tafi kasuwannin Najeriya, musamman Jibiya, Katsina da Kano, domin sayen kayayyakin da za su dawo da su Nijar su sayar. Sai dai a bayan wannan sana’a akwai ƙalubale da dama, waɗanda suka haɗa da tsadar kayayyaki, matsalolin sufuri da kuma yawan bincike da tsayawa a wurare daban-daban a kan hanya.

Kasuwacin zuwa  Najeriya dai  na daya daga cikin hanyoyin da Mata da dama ke samun kudin shiga  anan Maradi. Kama daga zuwa Magama, Jibiya Katsina har kano da su Mashi su mai Aduwa, babu kasuwannin da Matan ba su ci, yawancinsu ko dai Mazajensu sun mutu sun bar musu Marayu. Wasu kuma Jawaru ne dake dauke da nauyin kansu da na yayansu, wasu kuma da aurensu amma sune ke daukar dawainiyar gida.To sai dai akwai wahalhalu da dama musamman na kan hanya da kuma ta tsadar kaya da Matan ke fama da su a wannan lokacin dake zama kalubale  kafin cimma buri da matan su ka sa gaba. Laure wata mata ce mai shekaru 50 da take cin kasuwar Jibiya tace ta « fara wannan sana’a ta zuwa kasuwar Jibiya shekaru goma (10) da suka wuce. A da,  idan ka je da naira dubu ashirin, za ka iya sayo kaya har buhu guda. Amma yanzu ko da ka je da naira dubu ɗari, ba za ka iya sayen irin waɗannan kayan ba saboda tsadar rayuwa.Sannan akwai matsalolin hanya. Wasu mata suna biyan kuɗin hanya, wasu kuma ba sa biya. Idan ka biya ma, wani lokacin ana ci gaba da karɓar kuɗi a wurare daban-daban, har ya kai ka rasa kudin  hawa mota ka riƙa hawa babur ko adaidaita sahu.Wasu lokuta ma sai ka ci bashi kafin ka isa kasuwa»

Anata bangare Hajiya Aina’u wata uwar iyali mai cin kasuwar Kano ta  bayyana matsalar da suke fuskanta kan hanya, tana mai cewa.« Ina zuwa  kasuwar Kano ne. Da farko ba ita ce kasuwata ba, amma bayan Mai gindana ya yi ritaya daga Arlit mun dawo Maradi. Sai na yi tunanin irin kasuwancin da zan yi, na ga kasuwar Kano ce ta fi karɓuwa, saboda haka na fara zuwa can. Muna fuskantar matsaloli. Matsala ta farko ita ce a kan hanya. A cikin Nijar jami’an tsaro suna bincike ne kawai, amma idan ka isa kan iyaka sai ana karɓar kuɗi. Daga Magama zuwa Kano muna wucewa ta shingayen bincike kusan goma, kuma a kusan kowane wuri ana karɓar kuɗi ba tare da ba ka wata takarda ko rasit ba. »

Mata suna cin amfanin kasuwancin sosai

Sai dai kuma duk da wadannan wahalhalun da Matan ke fuskanta, Laure Sani ta ce wannan  sana’a tanada amfani a garesu. « Da ita muke siyen kayan makaranta da tufafi ga ‘ya’yanmu, muna kuma samar da abin ci ga iyali. Mu mata ba ma son ganin ‘ya’yanmu suna kwana da yunwa.Wahalhalun gida sun fi yawa a kan Mata, ko mace mai aure ce, bazawara  ko kuma mai kula da marayu. Idan ka duba hanyar Jibiya, a cikin motoci kusan mata ne mafi yawa. Wannan ya nuna irin ƙoƙarin da matan Maradi suke yi wajen neman abin dogaro.»

Duk da ƙalubalen da ke tattare da kasuwancin kan iyaka, mata masu safarar kaya tsakanin Najeriya da Nijar na ci gaba da jajircewa. Burinsu shi ne bunƙasa sana’arsu, inganta rayuwar iyalansu da kuma ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasarsu.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )