
Yadda siyar da fara ya zama sana’ar dogaro da kai ga wasu matan Maradi
A Maradi, wasu mata na gudanar da sana’o’i daban-daban domin samun abin dogaro da kuma tallafa wa iyalansu. Saude Abdou, wata mai sana’ar siyar da fara, wadda kuma uwa ce ga yara huɗu. tace kasuwancin siyar da far aya yi tasiri sosai a rayuwarta
Shekaru 22 kenan da Saude Abdu ke sana’ar siyar da fara, Ta ce sana’ar tana taimaka mata wajen biyan bukatun yau da kullum da kuma tallafa wa iyalinta.
« Ina da yara huɗu, kuma sana’ar fara na shafe shekaru 22 ina yin ta, Tun farko ina yin ƙananan sana’o’i daban-daban, amma daga baya na fi karkata ga sana’ar siyar da fara, saboda na lura cewa mutane suna son cin fara kuma ana samun riba a cikinta.Hakan ya sa na dage da ita, har na yi suna a wannan sana’a, na bar sauran sana’o’in.Idan na sayo fara a kasuwa , nakan kawo ta gida,daga nan sai a tsabtace ta, a shirya ta, sannan a soya. Abubuwan da ake buƙata wajen shirya fara sun haɗa da albasa, tafarnuwa, Maggi, attarugu da gishiri. Waɗannan su ne muhimman kayan da nake amfani da su»
Yawancin masu sana’a na kokawa da rashin masaya, ko yaya abin yak e ga malama Saude ?
« Kullum ina samun masu zuwa saye, amma mafi yawan lokaci ana zuwa sayen fara da dare, kuma nakan samu ciniki sosai. Har ma nakan je kasuwa da dare domin sayar da ita, musamman Litinin da Juma’a.Ina sayar da fara a kasuwar Ya Sonita da ke Maradi, da kuma kasuwar Tsibiri. Duk lokacin da na siyo fara, a ranar nake sayota , gobe kuma ta ƙare saboda yawan masu saye.»
Duk da nasarorin da ta samu Malama Saude ta bayyana wasu matsaloli dake zama babban kalubale a gareta sannan tayi kira da mata da matasa su rungumi sana’a komin kaden dinta.« Muna samun wasu matsaloli. Misali, wani lokaci idan na siyo fara wadda ba ta da kyau, hakan na iya jawo matsala. Idan mutum ya siya, ya ɗanɗana , ya ga ba ta da kyau, ba zai sake dawowa ba. »
Ta hanyar wannan sana’a malama Saude tace ta samu rufin asiri tare da kira ga yan uwanta mata da matasa.
« Ta hanyar wannan sana’a nakan samu abin da zan biya bukatuna, sannan har nakan iya taimakawa wasu daga cikin ’yan uwana.Burina a nan gaba shi ne in ƙara faɗaɗa sana’ar, musamman samun kasuwa mai kyau da za ta ba ni damar siyar da fara a wurare daban-daban, har ma mutane su riƙa zuwa yin oda. Ina kira ga mata masu son yin irin wannan sana’a da su rungume ta, domin sana’a ce mai kyau kuma tana taimaka mini sosai. A yanzu haka ina ƙoƙarin tara jari, na ƙara gyara sana’ar da kuma tanadin fara. Insha Allah, nan da shekaru biyar zuwa goma ina fatan samun babban jari da kuma faɗaɗa sana’ar. »
Yayin da mata da dama ke neman hanyoyin inganta rayuwarsu da ta iyalansu, sana’o’i irin na siyar da fara na ci gaba da kasancewa wata hanya ta samun kuɗin shig

