Abota, wata alaƙa mai muhimmanci da take ginuwa kan aminci da riƙe sirri.
Abota tana ginuwa ne sannu a hankali ta hanyar girmama juna, aminci da kuma rike sirri. Ga mutane da dama, samun abokai na gaskiya yana taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa ba tare da kasancewa su kaɗai ba.
Tsakanin aminci, taimakon juna da kuma bayyana sirruka, abota na taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum. A Maradi, wasu sun bayyana yadda waɗannan alaƙoƙi ke ƙara ƙarfi har su zama kamar dangantakar jini.
Abota tana ginuwa ne sannu a hankali ta hanyar girmama juna, aminci da kuma rike sirri. Ga mutane da dama, samun abokai na gaskiya yana taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa ba tare da kasancewa su kaɗai ba.
Haka lamarin yake ga Rayanatou, wadda a yau take kallon ƙawayenta a matsayin ‘yan uwanta na jini.
« Abota tana da muhimmanci sosai a rayuwata, domin ina da ƙawayen da muke raba komai tare. Suna sona da gaske, kuma suna tare da ni a lokacin farin ciki da kuma lokacin wahala. Da tafiyar lokaci, sun zama kamar ‘yan uwana mata. Yanzu ma ba ma kiran kanmu abokai kawai, muna kallon kanmu a matsayin iyali guda. » acewar ta.
Amincewa da bayyana sirri a cikin abota
Ga wasu kuma, ƙarfin abota yana cikin amincewa da juna da rikon sirri. A cewar Moustapha Illa , « daya daga cikin manyan alheran abota shi ne rabon sirri. Kamar yadda masoya ke bayyana soyayyarsu ga juna, ko abokan karatu ke musayar ayyuka, abokai na gaskiya kuwa suna bayyana wa juna sirrukan zuciyarsu. Wannan amincewa ita ce ginshiƙin abota ta gaskiya mai ɗorewa. »
Baya ga lokutan farin ciki da nishaɗi, abota tana zama tushen kwanciyar hankali da taimakon juna. Domin ta daɗe, dole ne ta kasance bisa gaskiya, mutunta juna, riƙon amana da kuma amincewa.

