1.	MATASALAR ALBUZARANCI DA ABINCI YAYIN BUKUKUWA A KARKARA.

1. MATASALAR ALBUZARANCI DA ABINCI YAYIN BUKUKUWA A KARKARA.

Barnar abinci yayin bukukuwa, kamar aure, suna da jana’iza, a yankunan karkara na Maradi, na daga cikin manyan matsalolin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu ga al’umma a kauyuka.

 

A ƙauyen El Tsamiyar da ke Mayahi, mata ne suka fi yin almubazzaranci da abinci a lokacin bukukuwa a cewar Mai gari, Sama’ila.

«Yin almubazzaranci da abinci ya wuce hankali, musamman a lokacin bukukuwan aure, inda ake yawan gudanar da shagulgula fiye da kima. A irin waɗannan lokuta, wasu iyalai kan dafa har buhunan shinkafa guda biyar domin tarbar baƙi, musamman mata mambobin ƙungiyoyin adashe, waɗanda kan zo da yawa domin halartar bikin.

Baya ga shinkafa, ana kuma amfani da gero mai yawa wajen yin tuwo, kunu da kuma fura. Ana samun irin wannan almubazzaranci musamman a lokacin ƙuncin abinci, wato lokacin da amfanin gona na shekarar da ta gabata ya ƙare, amma ba a fara girbin sabon amfanin gona ba. A daidai wannan lokaci ne kuma iyalai da dama ke fuskantar matsaloli wajen samun isasshen abincin da za su ci. »

 kashe kuɗaɗe  da barnar abinci fiye da kima a lokacin bukukuwa suna jefa iyalai cikin matsin tattalin arziki, har ma su sa su shiga bashi da kuma fuskantar asarar kuɗi mai yawa. Wanda kuwa ya saɓa da ainihin ƙarfin tattalin arzikin iyalai a karkara. »

Dangane da wannan matsala, mai garin El Tsamiyar da ke Mayahi, Sama’ila, yana amfani da mai shela domin wayar da kan al’umma tare da kira gare su da su daina wannan mummunar ɗabi’a ta almubazzaranci da abinci a lokacin bukukuwa.

« kai a kai, muna ƙoƙarin wayar da kan al’umma kan muhimmancin guje wa almubazzaranci da abinci a lokacin bukukuwa. Matsalar ita ce, wasu mata, ko da ba su da isassun kuɗi, ba sa shakkar shiga bashi domin gudanar da bukukuwansu. Suna sayen ledojin lemun kwalba da masara a bashi, da fatan za su biya bashin ta hanyar kyaututtuka da gudummawar da baƙi za su bayar .

Abin takaici, wani lokaci kuɗin da ake samu bayan an kammala bikin ba sa wadatar biyan kuɗin da aka kashe. A nan ne matsaloli ke farawa tsakanin masu bashi da waɗanda suka karɓi bashin.

Dangane da wannan matsala, nakan yi amfani da mai shela, wanda yake zagayawa cikin ƙauyen domin isar da saƙona ga al’umma. Yana tunatar da jama’a cewa mai gari yana kira ga kowa da kowa da ya kasance mai yin komai cikin matsakaici, ya guji kashe kuɗi fiye da kima, musamman ma kada mutum ya yi ƙoƙarin kwaikwayon masu hali alhali ba shi injishi.»

Wani Babban ɓangare na abincin da ba a ci ba yana ƙarewa ne a kwandon shara ko kuma a zubar da shi a banza, alhali kuwa wasu yankuna da iyalai na fuskantar matsalolin ƙarancin abinci da bukatar shi.

Ahadi Moussa

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )