Wayar da kan jama’a bisa illar cin zarafi a cikin zamatakewa.

Wayar da kan jama’a bisa illar cin zarafi a cikin zamatakewa.

Akwai bukatar matasa da mata su dinga ziyartar gidajen asibiti domin kula da lafiyarsu

Membobin Ratanga Club Niger sun gudanar da wani babban taron gangamin wayar da kai kan cin zarafin diya mata cewa da violence base sur le genre(VBG) da kuma sha’anin kiwon lafiyar a Cibiyar Matasa ta Garkuwa dake nan  Maradi unguwar Ali Dan Tsofo, a cikin ayyukan shirin Furuje  Rayuwa  C’est la Vie  Mataki na 2.

Wannan gamayar mambobin Ratanga Club, sun hada Lafiya Matasa, OSC, CAR/PF na Nijar, da kuma Cibiyar Gidajen Rediyoyin karkara ta Nijar, bisa tallafin RAES.

A cikin wanan tafiya membobin ratanga sun wayar da kan jama’a a fanonin da dama, daga cikin har da matasa,  mata da maza, masu unguwani, sarakunan  gargajiya da malaman addinin musulunci domin muntata jinsi da yaki da cin zarafi musamman ga diya mata, Malama Balki rabi’u daya daga cikin malaman na mai cewa.

«Da matasan da iyayen, a wannan karnin da muke, ya kamata mu kanmu mu sa ido kan diyan mu, saboda ana nan ana muzgunawa kananan yara musaman yan mata suna nan suna fuskantar fyade, don haka na cewa masu unguwani su suje bangaren maza mu muja wajan mata mu ci gaba da fadakar da jama’a kamin ake sake nemo mu. »

Daga ciki tafiyar akwai bukatar matasa da mata su dinga  ziyartar gidajen asibiti domin kula da lafiyarsu, shin ko wane tabbaci jami’an kiwon lafiya ke bayarwa wajan kare sirrin matasan, da zai janyo hankalinsu wajan debe shakkun kan boye sirrin su ?

Rayanatou  Gwanda  Kure dake sashen kula da lafiyar diya mata cewa da sage-femme a CSI kasum Muktar Zaria na mai bayar da tabbaci kamar haka.

« Shin babban abin da jami’in kiwon lafiya ya kamata ya fara ga mars lafiya shine tarbe kyaukyawa, saboda a cikin aikinmu an tabbatar da cewa idan maras lafiya  ya samu tarbe na gari, kaso 50% na ciwon ya samu magani, don haka nike kira ga matasa mata da maza suzo su bamu amanarsu, za mu rike ta, saboda dokar aikinmu ce na  boye sirin dan malati, don haka su bar jin shakku su yarda damu domin gidan asibiti ba abin kyama ba ne. »

A cikin tafiyar bayan gidajen Radiyo, membobin sunyi amfani da wasan kwaikwayo da kade kade da sauran wassannin da matasa ke bukata wajan isar da sako, Mariama Rabi’u wata matashiya da ta halarci wurin ta bayyana irin yadda taji bayan kallon wassanin.

« Abin da na fahimta kuma na dauka a cikin shine  na ga yadda bai kamata a dinga cin mutuncin mata ba, saboda a cikin wasan kwaikwayon an nuna yadda shi yake kokarin yake kuntatama iyalan shi, da wani salo a karnin da ya wuce, alhali yanzu an waye.kuma naga yadda aka nuna ba a ba matasa damar zabin abinda suke so a ran su.Wanan bai yi ba don haka yanzu ya kamata kowa ya sani zamani yazo kuma lokaci ya sauya.Don haka muna kira ga iyaye su janyo diyan su ga jiki Kuma su dinga basu zabi kan rasuwar su. »

Manufar wannan tafiya itace  samun sauyin tunani domin shawo kan wannan matsalar ta cin zarafi da daidaita zamantakewa ko jinsi tsakanin alumma.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )