
Saka abinci mai zafi cikin leda: Barazanar da ke tattare da lafiyar masu amfani da shi.
wasu sinadarai na iya kasancewa da alaƙa da matsalolin da suka shafi sinadaran hormones, haihuwa, hanta, ƙoda da tsarin jijiyoyin ƙwaƙwalwa.
Daga shinkafa zuwa wake, da kuma tuwon da aka yi da kullu ko kunu, ana yawan amfani da ledar roba wajen zuba abinci a Nijar, har ma idan abincin yana da zafi. Wannan al’ada ta zama ruwan dare a kasuwanni, rumfunan sayar da abinci da kuma tituna. Sai dai masana na gargadin cewa wannan dabi’a na iya haifar da matsaloli ga lafiyar jama’a da kuma muhalli.
Ga yawancin masu sayarwa da masu sayen abinci, leda hanya ce mai sauƙi, arha kuma mai sauƙin ɗauka. Sai dai idan aka zuba abinci mai zafi kai tsaye cikin ledar roba, wasu sinadarai da ke cikin ledar na iya shiga cikin abincin.
A cewar Dakta Mahaman Daha Daouda Ali, masani kan lafiyar jama’a, zafin abinci na daga cikin abubuwan da ya kamata a kula da su. «Idan abinci mai zafi ya taɓa leda, wasu daga cikin sinadaran da ke cikin ledar na iya fita su shiga cikin abincin Shigar wasu daga cikin waɗannan sinadarai cikin abinci na iya haifar da damuwa ta fuskar lafiya, musamman idan mutum yana fuskantar hakan akai-akai. Dangane da nau’in ledar, zafin abincin, tsawon lokacin da abincin ya yi cikin ledar da kuma yawan amfani da ita, wasu sinadarai na iya kasancewa da alaƙa da matsalolin da suka shafi sinadaran hormones, haihuwa, hanta, ƙoda da tsarin jijiyoyin ƙwaƙwalwa. » in ji Dakta Mahaman Daha Daouda Ali.
Saboda haka, ya zama wajibi a kula da irin kayan da ake amfani da su wajen zuba abinci mai zafi, musamman abincin da ake sayarwa a kan tituna.
Akwai hanyoyin da za su maye gurbin ledar roba :
Domin rage irin wannan haɗari, Dakta Mahaman Daha Daouda Ali ya shawarci masu sayarwa da masu amfani da abinci da su koma ga wasu kayan da suka fi dacewa da zuba abinci mai zafi.
« Akwai hanyoyi daban-daban da za a iya amfani da su, kamar mazubi na takarda, mazubi na kwali da aka ƙera domin abinci mai zafi, kwalabe ko mazubi na gilashi, da kuma mazubi da ake iya amfani da su sau da yawa. Waɗannan hanyoyi suna rage taɓa abinci mai zafi da wasu nau’o’in ledar roba kai tsaye » in ji masanin.
Wannan shawara na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Nijar ke ƙara ɗaukar matakai kan amfani da leda. A birnin Yamai, Mai kula da harkokin birnin Yamai ya sanya hannu kan ƙuduri mai lamba 0071/AD/VN/SG a ranar 1 ga Yuli 2026, wanda ya haramta wasu nau’o’in ledar roba a manyan kantuna.
Matakin ya tanadi wa manyan kantunan wa’adin sauyi har zuwa 31 ga Disamba 2026, domin su daina amfani da irin waɗannan ledodin tare da komawa ga wasu hanyoyi kamar jakunkunan da suke narkewa cikin sauƙi, kwantena na takarda da kuma kwantena da ake sake amfani da su.
Sai dai aiwatar da dokokin kaɗai ba zai wadatar ba. Ana buƙatar wayar da kan masu sayarwa da masu sayen abinci, ƙara sa ido kan irin kayan da ake amfani da su wajen zuba abinci, da kuma samar da wasu hanyoyin da za su kasance masu sauƙi da araha.

