
Maradi: Majalisar Matasa ta shirya gangamin wayar da kan al’umma kan tsafta a Mazadu Jika.
“Babban burinmu shi ne mu sa al’umma su taka rawa wajen inganta ayyukan gwamnati, musamman a fannin kiwon lafiya da tsaftar muhalli.”
Majalisar Matasan Shiya ta Ɗaya ta birnin Maradi ta shirya wani gangamin wayar da kan al’ummar unguwar Mazadu Jika kan muhimmancin tsafta da kuma yin amfani da cibiyoyin kiwon lafiya, musamman a wannan lokacin damina.
Unguwar Mazadu Jika na daga cikin unguwannin da ke fuskantar matsalolin tsaftar muhalli a birnin Maradi. Wannan yanayi na iya ƙara haɗarin barkewar cututtuka idan ba a ɗauki matakan kariya da suka dace ba. An shirya wannan gangami ne domin tunatar da al’umma kan hanyoyin kare kai daga cututtukan da ke da alaƙa da rashin tsafta, waɗanda suka haɗa da kwalara da zazzabin cizon sauro, musamman a lokacin damina.
Shugaban Majalisar Matasan Shiya ta Ɗaya, Abdou Rahamane Halidu Issa, ya bayyana cewa babban burinsu shi ne ganin al’umma ta taka rawa wajen tallafa wa ayyukan gwamnati, musamman a fannin kiwon lafiya da tsaftar muhalli. “Babban burinmu shi ne mu sa al’umma su taka rawa wajen inganta ayyukan gwamnati, musamman a fannin kiwon lafiya da tsaftar muhalli.” A cewar sa.
Ya ƙara da cewa suna fatan mazauna unguwar za su ci gaba da ba da haɗin kai, tare da aiwatar da shawarwarin da ƙwararrun ma’aikatan lafiya da jami’an kula da tsaftar muhalli suka ba su, musamman wajen kiyaye tsaftar harabar Cibiyar Kula da Lafiya (CSI) da sauran wuraren da jama’a ke amfani da su.
A nasa ɓangaren, Mahi Lawali, ɗaya daga cikin matasan unguwar, ya ce taron ya taimaka wajen ƙara fahimtar muhimmancin tsafta, inda ya ɗauki alƙawarin bayar da gudunmawa wajen tsaftace muhalli: “Tabbas, a wannan taron mun koyi abubuwa da dama, musamman abubuwan da suka shafi tsafta. Mun kuma yaba da wannan shiri na Majalisar Matasa, musamman a wannan lokacin damina.” a cewar sa.
Ya ƙara da cewa matasan unguwar za su yi ƙoƙarin amfani da abin da suka koya wajen inganta tsaftar muhalli da kuma wayar da kan sauran jama’a.
Masana kiwon lafiya na jaddada cewa kiyaye tsafta na daga cikin muhimman hanyoyin kare kai daga cututtuka, musamman a lokacin damina.
Madam Sani Nana Fatchima Adam, mai kula da gidan haihuwa na asibitin Mazadu Jika, ta yi kira ga jama’a da su ƙara kula da tsaftar hannu, abinci da muhalli domin rage yaɗuwar cututtuka.
Ta ce cututtukan da ake iya samu ta hanyar ruwa kan yaɗu sosai a lokacin damina, don haka ya zama dole jama’a su riƙa wanke hannayensu, musamman kafin cin abinci, tare da wanke kayan abinci da kyau kafin amfani da su.
Ta kuma shawarci jama’a da su tabbatar da cewa abinci an shirya shi kuma an dafa shi yadda ya kamata, sannan a kare shi daga gurɓacewa. Haka kuma, ta jaddada muhimmancin amfani da bandaki yadda ya kamata da kuma kiyaye tsaftarsa.
An gudanar da wannan gangami ne tare da tallafin SOS Civisme au Niger, a matsayin wani mataki na rigakafi bisa karin maganar Hausawa cewa “rigakafi ya fi magani.”
Masu shirya taron sun bayyana cewa irin waɗannan ayyukan wayar da kan jama’a na da matuƙar muhimmanci, musamman ganin yadda wasu unguwannin Maradi ke fuskantar haɗarin barkewar cututtuka a lokacin damina. Don haka, an yi kira ga mazauna Mazadu Jika da sauran al’ummar birnin Maradi da su haɗa hannu wajen kiyaye tsaftar muhalli, amfani da hanyoyin kariya daga cututtuka, da kuma gaggauta zuwa cibiyoyin kiwon lafiya idan an samu alamun rashin lafiya.
Illia Moumouni.

