Saudiyya ta sanar da ranekun aikin Hajjin 2027

Saudiyya ta sanar da ranekun aikin Hajjin 2027

Ga masu kamfanonin aikin hajjin daukar wannan mataki akwai hujja .

Kasar Saudiyya ta fitar da sabon jadawalin ne a takaitaccen lokaci banban da shekarun baya. Za a kawo karshen rubuta sunayen maniyyata a ranar 26 ga watan Satumban 2026, yayin da biza zata fara fita a watan janairu sai tashin farko ta hanyar jirgi a watan Afirilu. Wannan sabon tsarin dai zai sa kamfanoni aikin Hajji su zage damtse wajan waye kan maniyyata.

Ga masu kamfanonin aikin hajjin daukar wannan mataki akwai hujja .

« A yan shekarun nan al’ummar musulmin dake son gudanar da aikin hajji na kara yawa, yayin da wuraren ibada ake kara samun cinkoso, shiyasa Saudiyya ke son yin zagin gaba wajan shirya aikin a tsanake. Sabon tsarin da aka kawo shekaru biyun da suka gabata, shine duk wasu mazauna Makkah da basu cikin tsarin aikin Hajjin zasu bar garin har sai an kare su dawo.idan suka zauna tare da maniyyata zai haddasa matsalolin cinkoso da zirga zirgar ababen hawa. Don haka Saudiyya ke bukatar sanin adadin maniyyata tun da wuri don yin tsari mai kyau», Inji Alhaji Isufu Mamman na kamfanin  Godiya. 

Guzuri Hajji wani lokaci nayin kadan

Domin magance matsalolin da zasu sa rashin tafiya, dole maniyyaci ya bi ka’idojin da kasar Saudiyya ta shimfida, ya tanadi takardun balaguro kan lokaci, sannan da bin tsarin da aka saka.hakanan dole maniyyaci ya tanadi isassun kudi na guzuri a duk lokacin da zai kasance a kasar ta Saudiyya Fadar Alhaji  Isufu Mamman na kamfanin Godiya.

 «Akwai mutanen dake biyawa iyaye ko yan uwansu kujera, amma su basu yan kudi kalilan na guzuri kamar Cfa jika dari da hamsin zuwa jika dari uku, alhali ko cfa jika dari biyar bata isa saboda a yanzu abinci na tsada sai cikin gidajen siyar da abinci ake samunsa babu irin namu na gargajiya bayan fage saboda an kori mutanen daga cikin garin Makkah. Wannan kuma babbar matsala ce. »

Duk da cewa wasu maniyyatan sun biya kujerarsu, amma sukan rasa samun tafiya saboda latti wajan rubuta suna, don haka ya zama wajibi ga kamfanoni su zafafa waye kan al’umma domin rubuta suna da wuri.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )