
Maimuna: Mai sayar da kayan bocho tsawon shekaru 22.
“Maganin zaman banza, ina zaune a gida ga yara, shi ya sa na shiga sana’ar sayar da bosho. Sannu a hankali na fara. Da farko kaɗan nake saya, har na fara samun damar ɗauko kaya da yawa,”
A cikin kasuwannin birnin Maradi, mata da dama na dogaro da sana’ar sayar da kayan bosho domin samun abin dogaro da kai da kuma tallafa wa iyalansu. Daga cikin su akwai Maimuna, uwa mai ’ya’ya bakwai, wadda ta shafe shekaru 22 tana wannan sana’a.
Sana’a domin guje wa zaman banza
Maimuna ta ce ta fara sana’ar sayar da kayan bosho ne domin ta samu abin yi yayin da take kula da ’ya’yanta a gida.
“Maganin zaman banza, ina zaune a gida ga yara, shi ya sa na shiga sana’ar sayar da bosho. Sannu a hankali na fara. Da farko kaɗan nake saya, har na fara samun damar ɗauko kaya da yawa,” in ji ta.
A halin yanzu, tana sayar da kayayyaki daban-daban da suka haɗa da kayan yara, T-shirt, kayan mata masu ciki, barguna da sauran kayayyaki. Ta ce tana sayen kayan ne wajen ’yan dila da ke kawo kayayyakin su kasuwa.
A cewarta, kayan yara na daga cikin kayayyakin da ake saye sosai. Wasu abokan ciniki kan kira ta har gida domin ta kai musu kaya, yayin da wasu kuma daga garuruwa daban-daban ke sayen kayanta.
Sai dai Maimuna ta bayyana cewa kasuwa ba ta yin armashi a kowane lokaci. A cewarta, lokacin kaka shi ne lokacin da ake samun ciniki mai yawa, saboda yawan bukatar kayan sawa da sauran kayayyaki.
Hauhawar farashi da matsalar bashi
Duk da muhimmancin da sana’ar ke da shi a rayuwarta, Maimuna na fuskantar wasu ƙalubale, musamman matsalar karɓar bashi daga wasu masu saye da kuma hauhawar farashin kayan bosho.
“Gaskiya, akwai matsaloli. Wani lokaci mutum zai zo ya sayi kaya har gida, ya ce zai bayar da kuɗi daga baya, sai ka ji shiru idan lokacin biya ya yi. An sha cinye mana kuɗi sosai,” ta bayyana.
Ta kuma ce hauhawar farashin kayan da ake sayarwa na rage ribar ‘yan kasuwa. A cewarta, T-shirt da a baya ake sayarwa da dala 50 zuwa 60, yanzu farashinsa ya kai dala 160. Haka kuma, farashin wando na yara da kayan mata masu ciki ya ƙaru.
Duk da waɗannan ƙalubale, Maimuna ta ce sana’ar tana taimaka mata wajen samun abin da za ta ci da sha, sutura da kuma biyan wasu bukatun iyalinta.
Ta shawarci mata da su guji zaman banza, su nemi sana’ar da za su iya yi domin dogaro da kansu.
“Zaman banza ba yada amfani. A tashi a yi sana’a, ko da mijinki ya hana ki, ko a cikin gida ne, ki yi sana’a. Domin idan kika yi sana’a, kina da abin da kika mallaka da kanki,” in ji Maimuna.
Shekaru 22 da Maimuna ta shafe tana sana’ar sayar da kayan bosho sun zama shaida ta jajircewa, haƙuri da kuma dagewa wajen neman abin da za ta tallafa wa kanta da ’ya’yanta bakwai. A gare ta, sana’ar ba kawai hanyar samun kuɗi ba ce, har ila yau hanya ce ta gina makomar iyalinta.
Roumanatou Harou.

