
Yadda za’ayi riga kafin cutar shawara ko ciwon anta.
Cutar shawara na da sanfuri iri daban daban a likitance. Shawara ko kuma bayyama mai sanfurin A mafi yawa ana daukar tane ta mu’amala da ruwa ko abinci marar tsabta. Ana samun launin wannan cuta musamman inda tsabta tayi karanci. Dr Manu na likitar kaura Hassaw dake nan Maradi ya bayyana yadda ake riga kafin ta :
Cutar anta ko shawara mai saurin yaduwa nau’ikan A, B da kuma C na daga cikin manyan matsalolin kiwon lafiyar jama’a a Nijar. Ana iya kamuwa da wadannan cututtuka ta hanyoyi daban daban, kuma suna iya lalata hanta tare da haifar da manyan matsaloli ga lafiya, har ma damutuwa idan ba’a gano su da wuri ba da kuma kulawar da ta dace.
Cutar shawara na da sanfuri iri daban daban a likitance. Shawara ko kuma bayyama mai sanfurin A mafi yawa ana daukar tane ta mu’amala da ruwa ko abinci marar tsabta. Ana samun launin wannan cuta musamman inda tsabta tayi karanci. Dr Manu na likitar kaura Hassaw dake nan Maradi ya bayyana yadda ake riga kafin ta :
« Shawara mai rukunin A, ana daukar kwayoyin cutar ne ga abincin da muke ci. Dan haka duk abincin da zamu ci ya dace mu tabbatar cewa mai kyau ne. Saboda idan muka ci abincin marar kyau to akwaiyiyuwar zamu iya kamuwa da cutar shawara mai rukunin A ».
Samar da kariya daga cutar shawara mai rukunin B da C
Shawara ko bayyama mai sanfurin B da kuma C su kuma ana daukar sune ta hanyar jini, zuha, miyau, maniyi ko makamanci haka masu dauke da kwayar cutar. Yayin da a bangare guda uwa zata iya sa wa danta cutar a yayin haihuwa haka zalika jima’i ba tare da wata kariya ba ko aiki da allura mai dauke da kwayar cutar sukan iya kasancewa sanadiyyar kamuwa da cutar. A cewar Dr Manou Amadou ana iya kare kai daga cutar.
« Ita kuma shawara ko bayyama mai rukunin B da kuma C ana kamuwa da su ne kamar yadda ake kamuwa da cutar SIDA ko HIV. Mafi yawa wajen jima’i ne ko saduwa ko kuma a saka wa mutum jini wanda ke dauke da kwayoyin wannan cutar. Kenan ùe ya kamata mutum yayi idan har yana son yayi riga kafin irin nau’in wannan shawara shine kar mutum yayi jima’i cikin hadari wato ba tare da kariya ba. Matukar akwai hadari, to kuma tabbas akwai hadarin kamuwa da wannan rukunin cutar shawara, sannan ita kuma fa mun san bata da magani kuma tunda babu magani to a dauki matakan riga kafin cutar. Sannan yana da kyau duk wadanda zasu yi aure to su je su yi gwajin jini don kaucewa kamuwa da kwayoyin cutar shawara. Idan kuma mutum yaki wannan dan kan shi. »
Yaki da cutar shawara ko bayyama ko kuma ciwon anta, zai fara ne daga waye ma al’umma kai bisa hanyoyin kamuwa da cutar da kuma aiki da matakan kariyar kanshi. Yana da kyau muyi binciken jini kafin aure kuma muyi taka tsantsan saboda cuta ce mai illa sosai ga rayuwarmu.

