Tsaftar Jinin Haila : Muhimmin Batu ne na Lafiyar Mata da ’Yan Mata a Maradi.

Tsaftar Jinin Haila : Muhimmin Batu ne na Lafiyar Mata da ’Yan Mata a Maradi.

A Maradi, har yanzu ana kallon batun jinin haila a matsayin abin da ya kamata a yi shiru a kai. Duk da haka, haila wata dabi’a ce ta halitta da mata da ’yan mata masu balaga ke fuskanta a kowane wata. Domin kare lafiya, ungozoma ta jaddada muhimmancin tsaftar lokacin haila da kuma wayar da kan ’yan mata tun kafin su fara jinin hailarsu na farko.

 

A kowane wata, mata da ’yan mata da dama kan fuskanci lokacin haila. Sai dai duk da kasancewarta wata dabi’a ta halitta, har yanzu batun haila na fuskantar rashin samun damar magana a kai cikin ’yanci a wasu iyalai da cikin al’umma.

Wannan yanayi na iya haifar da karancin ilimi ga ’yan mata game da hanyoyin da ya kamata su bi wajen kula da tsaftarsu a lokacin haila.  Kiyaye tsafta yadda ya kamata na taimakawa wajen rage wasu matsalolin lafiya da kuma ba mata damar gudanar da wannan lokaci cikin kwanciyar hankali.

Sauƙaƙan matakai na kiyaye tsaftar lokacin haila

A cewar  malama Soumaila Marie, ungozoma a likita CSI 17 Portes ta Maradi, akwai nau’o’in kayayyakin kariya da mata za su iya amfani da su a lokacin haila .  “Domin tabbatar da tsaftar al’aura a lokacin haila, akwai kayayyaki daban-daban da za a iya amfani da su, musamman auduga, zanen kariyar haila da sauran kayayyakin da ake zubarwa bayan amfani,” in ji ta.

Ta kuma jaddada muhimmancin wanke hannu kafin kula da al’aura da kuma sauya kayan kariya a kai a kai.

“Abu mafi muhimmanci shi ne a tsaftace wajen al’aura da hannu mai tsabta, sannan a riƙa sauya kayan kariya akai-akai, musamman duk bayan sa’o’i huɗu zuwa takwas,” ta bayyana. Ta ƙara da cewa idan mace na zubar da jini mai yawa, ya kamata ta sauya kayan kariyar kafin wannan lokaci.

Rashin tsafta na iya ƙara wasu matsalolin lafiya

Rashin isasshen bayani da kuma wasu munanan halaye na tsafta na iya jefa mata cikin haɗarin fuskantar wasu matsalolin lafiya. Saboda haka, malama Soumaila Marie ta yi kira da a riƙa bin matakan tsafta a duk tsawon lokacin haila.

“ Mutuncin mace yana cikin lafiyarta ta jima’i,” in ji ta. Ta ƙara da cewa, “idan ba a kula da tsafta yadda ya kamata a lokacin haila ba, haɗarin kamuwa da wasu cututtuka na iya ƙaruwa. Saboda haka, yana da muhimmanci a riƙa bin ƙa’idojin tsafta a wannan lokaci,” ta jaddada.

Kada a yi watsi da ciwon mara a lokacin haila

Baya ga batun tsafta, wasu mata na fuskantar matsanancin ciwo a lokacin haila, wanda kan iya shafar harkokin yau da kullum.

“Wasu mata na fama da ciwon haila. Wani lokaci ciwon na iya kawo cikas ga rayuwarsu ta yau da kullum, kuma idan ciwon ya yi tsanani ko kuma ya kasance ba irin wanda aka saba gani ba, ya kamata a nemi kulawar ma’aikatan lafiya,” ta yi bayani.

Ta kuma yi kira ga mata da kada su ɗauki matsanancin ciwon haila da wasa, musamman idan ciwon ya kasance mai tsanani, ba a saba da shi ba ko kuma yana ci gaba da maimaituwa.

Kira ga iyaye mata da su wayar da kan ’ya’yansu

A cewar ungozomar, ya kamata a fara koyar da ’yan mata tsaftar haila tun kafin su fara ganin jinin haila na farko.

“Ina kira ga iyaye mata da su fara wayar da kan ’ya’yansu tun kafin su fara haila, game da muhimmancin tsaftar lokacin haila da kuma kyawawan halayen da ya kamata su riƙa bi a wannan lokaci,” in ji ta.

A cewarta, irin wannan wayar da kai tun da wuri zai taimaka wa ’yan mata wajen fahimtar sauye-sauyen da ke faruwa a jikinsu da kuma kasancewa cikin shiri lokacin da suka fara haila.

A Maradi, tsaftar lokacin haila na ci gaba da kasancewa wani muhimmin batu da ya shafi lafiya da ilimi. Samun ruwa mai tsafta, kayan kariya da suka dace da kuma ingantaccen bayani na daga cikin abubuwan da za su taimaka wa mata da ’yan mata wajen gudanar da lokacin haila cikin yanayi mai kyau.

Aicha Ousmane.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )