Yadda mata a Maradi, ke ci gaba da tururuwa wajen koyon kananan sana’o’i don su dogara da kansu.

Yadda mata a Maradi, ke ci gaba da tururuwa wajen koyon kananan sana’o’i don su dogara da kansu.

Ina da yakinin muddin ka koyi aikin hannu to jazaman ne ba zaka rasa abin yi ba

A Maradi, mata da dama yanzu haka na zuwa dakunan daukar horo ko foyer domin koyon kananan sana’o’i domin tallafawa y’an uwansu, y’ay’ansu da kuma mazajen su. Hakan na basu damar dogaro da kansu idan sun girku kan sana’o’in da suka koya.

Zaune kan keken dinki rike da wata y’ar karamar riga, malama Halima Gusmane y’ar shekaru arba’in da y’an kai ta tarbe mu cike da fara’a. Mace mai cike da kwarjini, ta bayyana cewa dawainiya da kuma nauyin iyali da yayi wa maigidanta yawa ne ya sa zo wani dakin koyon kananan sana’o’i mai suna foyer alheri don ta koyi aikin da kuma girkin zamani.

«  Yau da gobe sai Allah, namiji da yayi aure, iyali karuwa suke yi. Yau an haihu, jibi an kara samun karuwa, sannan ga dawainiya da darga ta dangi ga ta iyaye, don haka dole ka tallafawa kanka da kuma  y’ay’anka. To ka ji dalilin da ya sa na zo wannan foyer don na koyi sana’a »

Djamila Ibrahim y’ar kimanin shekaru 30,  wata matar gida ce dake zaune anan Maradi ita kuma kadaici da rashin aikin yi wajen samun dari da kobo ne ya sa ta shiga foyer don koyon dinki da kuma hada sarkoki domin ta taimaki kanta da kanta.

« A da zaune nike gida ba aikin da nake yi. Daga baya sai na ji labarin wannan foyer ta alheri inda aka tabbatar min ana aiki sosai. Ina da yakinin muddin ka koyi aikin hannu to jazaman ne ba zaka rasa abin yi ba. Sannan kafin ka tambayi mijinka neman wani taimako, to kai tuni ka biya bukatarka, da kuma ta danginka. Dan haka ina kira ga mata y’an uwana da su tashi tsaye domin dogaro da kansu, ba sai sun aza ma wani nauyi ba. Aikin hannu gaskiya yana da matukar amfani ga mata. Sakamakon aikin hannun da nake yi na taimaki y’an uwana da kuma y’ay’ana. Hatta kannena mata da suka yi aure ni na dinka musu zannuwan aurensu. Yanzu haka y’ay’ana ni da kaina ke yi musu dinki ba sai na kaiwa wani tela ba »

Suma masu bayar da horo suna alfahari da ci gaban da mata suke samu ta hanyar koyon wadannan kananan sana’o’i. Mme Hawa Omar Maman, wata mai bayar da horo ce a foyer Alheri ta bayyana farin cikinta na yadda mata ke turuwar zuwa koyon ayyuka don dogaro da kai. Ta kara da cewa da yawa sun samu shaidar kammala horon da suka samu a fanni daban daban inda da dama wasu suka fara aiki tare da burin samun incin samar da sana’ar kansu.

« Daga cikin mata dari biyu da hamsin dake koyon kananan sana’o’i wajen mu anan foyer Alheri, akalla 190 sun samu shaidar kamalla daukar horonsu tare da samun kayan aikinsu. Kuma a yau suna ci gaba da moriya da aikin da suka koya kumasuna tallafawa iyalinsu akan haka. »

Wadannan mata tabbas ba wai kawai kaya ne  suke dinkawa ba, a’a za’a iya cewa sun dauko wata hanyar gina rayuwar iyalinsu ne domin samar musu madogara.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )