
Damina: Iyalai a Maradi sun tashi tsaye wajen dakile yawaitar sauro.
<< Kare lafiya yana daga cikin muhimman nauyin da ke kan kowane shugaban iyali. Shi ya sa a wannan lokacin damina muke amfani da hanyoyi daban-daban domin kada mu bai wa sauro damar hayayyafa. Daga cikin hanyoyin da muke amfani da su akwai share ciyawa a cikin gida da kuma kewayen gida >>
Yayin da damina ta kankama, ruwa da ke tsayawa a cikin ramuka da kuma wuraren da ba a tsaftace su yadda ya kamata na samar da yanayi mai kyau ga yawaitar sauro. A Maradi, wasu iyalai sun mayar da hankali wajen tsaftace gidajensu da kewaye, domin rage wuraren da sauro ke yin ƙwai da hayayyafa.
Tsaftace muhalli, mataki na farko wajen yaƙi da sauro :
A wasu gidaje, yaƙi da sauro yana farawa ne da matakai masu sauƙi kamar share ciyawa, tsaftace harabar gida, zubar da ruwan da ya tsaya da kuma cike ramukan da ka iya tara ruwan sama.
Issoufou Idi Mahaman Sabiou, uban iyali, ya ce yana ba da muhimmanci sosai wajen tsaftace muhallin gidansa. << Kare lafiya yana daga cikin muhimman nauyin da ke kan kowane shugaban iyali. Shi ya sa a wannan lokacin damina muke amfani da hanyoyi daban-daban domin kada mu bai wa sauro damar hayayyafa. Daga cikin hanyoyin da muke amfani da su akwai share ciyawa a cikin gida da kuma kewayen gida >> in ji shi.
Ya ƙara da cewa, baya ga tsaftace muhalli, yana amfani da maganin kashe ƙwari tare da wayar da kan iyalinsa da maƙwabta. <<Ina kuma fesa gidan da maganin kashe ƙwari duk mako. Haka kuma ina gudanar da zaman wayar da kan ’yan uwa kan amfani da gidan sauro mai magani, tare da wayar da kan maƙwabta. Domin babu amfani mutum ya yi yaƙi da sauro a gidansa shi kaɗai, alhali sauro yana iya motsawa daga wannan gida zuwa wani, >> in ji Issoufou Idi Mahaman Sabiou.
Yanke rassan bishiyoyi da rufe ramuka :
A wasu gidajen kuma, ana amfani da yanke rassan bishiyoyi da kuma cike ƙananan ramuka domin hana ruwan sama taruwa. Wadannan matakai na taimakawa wajen rage wuraren da sauro ke iya yin ƙwai da hayayyafa.
Moustapha Illa, shi ma uban iyali, ya ce yana fara waɗannan ayyuka tun kafin damina ta fara, domin hana samuwar wuraren hayayyafar sauro. “Hanyar da nake amfani da ita tun kafin fara damina wajen yaƙi da wuraren da sauro ke hayayyafa ita ce yanke rassan bishiyoyin da ke cikin gida. Bayan haka, ina cike ƙananan ramuka da sauro zai iya yin ƙwai a cikinsu,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa wani lokaci yana amfani da magungunan kashe ƙwari domin ƙara ƙoƙarin kawar da wuraren hayayyafar sauro.
A Maradi, irin waɗannan matakai na nuna cewa yaƙi da sauro ba wai aikin hukumomin lafiya kaɗai ba ne. Tsaftace muhalli, kawar da ruwan da ya tsaya da kuma cike ramuka na daga cikin muhimman matakan da iyalai za su iya ɗauka domin rage yawaitar sauro, musamman a lokacin damina.

