
Babban hutu a Maradi: A gonaki, iyaye na dora muhimmanci kan tarbiyya da shagaltar da yara.
“ Wannan batun tarbiyya ne. Duk wanda Allah Ya azurta shi da ɗa, ya kamata ya koya masa ayyukan da za su amfanin rayuwarsa ”
A Maradi, lokacin babban hutun makaranta ba lallai ne ya kasance lokacin zaman banza ga yara ba. Yayin da makarantu ke rufe kofofinsu, wasu iyaye kan tafi da ‘ya’yansu gonaki domin su shiga wasu ayyukan noma. A wurin su, wannan hanya ce ta tarbiyya, koyar da sana’a da kuma kula da lafiyar yara da tsaronsu.
Noma a matsayin hanyar tarbiyya da koyarwa :
A raayin malan Makao, mai shekaru sama da 60 kuma mazaunin birnin Maradi, kai yara gona a lokacin hutu wani bangare ne na tarbiyya.
“Wannan batun tarbiyya ne. Duk wanda Allah Ya azurta shi da ɗa, ya kamata ya koya masa ayyukan da za su amfanin rayuwarsa,” in ji shi.
A cewarsa, iyaye suna da alhakin koyar da ‘ya’yansu ayyukan da za su iya taimaka musu a rayuwa. Baya ga koyon aikin noma, zuwa gona na ba yara damar sanin dukiyar iyalinsu da kuma filayen da suke mallaka.
Ya ce yana da muhimmanci yara su san inda gonakin iyalinsu suke, iyakokinsu da kuma bambancin su da na makwabta.
Ya kara da cewa :“Idan kuna tare da su, za su bi ku, kuma hakan yana ba ku damar sanya ido a kansu yadda ya kamata,”.
Shagaltar da yara domin kare su daga hadari
Ga wasu iyaye, kai yara gona a lokacin hutu ba wai koyar da aikin gona kawai ba ne, har ma wata hanya ce ta kare su daga wasu matsaloli.
A wasu yankunan Maradi, inda iyalai ke zaune kusa da gonaki da wuraren ruwa, wasu iyaye na ganin cewa barin yara ba tare da abin yi ba na iya sa su yawo ko kuma su shiga cikin wasu abubuwan da ba su dace ba.
Gambo Hamidu na daga cikin iyayen da ke tafiya gona tare da ‘ya’yansu.
“Lallai muna zuwa gona tare da yaranmu. Muna kai su ne domin kada su rika yawo daga wannan gona zuwa waccan, ko kuma su shiga gonakin wasu,” ya bayyana.
A cewarsa, yara kan shiga wasu ayyukan gona da suka dace da shekarunsu, kamar cire ciyawa da taimakawa wajen shuka. Wadannan ayyuka na ba su damar koyon dabarun noma da kuma sanin al’adun aikin gona da aka gada daga kakanni,iyaye zuwa ‘ya’ya.
Ya kuma bayyana cewa barin yara su kasance ba tare da kulawa ba a lokacin hutu na iya sanya su fuskantar munanan halaye ko kuma shiga cikin wasu dabi’un da ba su dace ba.
Hutu tsakanin noma, karatun addini da sada zumunci.
Saboda haka, ga wasu iyaye a Maradi, aikin gona a lokacin babban hutu wata dama ce ta ci gaba da tarbiyya da koyar da yara sana’o’in rayuwa, tare da tabbatar da cewa suna cikin wani yanayi na kulawa.
Sai dai aikin gona ba shi ne kadai abin da wasu yara ke yi a lokacin babban hutu ba. Wasu na ci gaba da zuwa makarantun allo domin karatun Alkur’ani mai girma da sauran ilimin addini. Haka zalika wasu iyayen, musamman mazauna birane na tura ‘ya’yansu garuruwansu na aihuwa domin sada zumunci da kuma daukar darussa game da halin zamantakewar rayuwa a karkara .

