Gudunmuwar kungiyoyin matasa wajen  yaki da matsalolin shaye shaye, rashin aiki da kuma rashin tsaro a jahar Maradi.

Gudunmuwar kungiyoyin matasa wajen  yaki da matsalolin shaye shaye, rashin aiki da kuma rashin tsaro a jahar Maradi.

Mun yi wani rangadi da muka wayewa matasa kai a cikin commune ko kananan hukumomi guda biyar dake yankin Gidan Roumdji tare da gudunmowar majalisar shawara na wadannan kananan hukumomi.

Sakamakon ranar matasa da majalisar dinkin duniya ta ware a kowace ranar 12 ga watan August, ya sa muka yi waiwaye kan gudun mowar da kungiyoyin matasa ke bayar wa wajen wayar da kan matasa don warware matsalolin da suka shafi harakar shaye shaye, rashin tsaro da kuma rashin aikin yi.

A yankin Gidan Roumdji, matasa na shirya tarurruka don wayar da kan matasa musamman kan hadarin shaye shaye da kuma harakar rashin tsaro. Yacouba Labo shine shugaban majalisar matasa na yankin Gidan Roumdji ya bayyana cewa« A matsayinmu na shugabannin majalisar matasa muna fafutuka don kawo tamu gudunmo musamman kan abinda ya shafi tsaro da tu’ammali da miyagun kwayoyi wanda matasa ke yi. Sanin kowa ne idan aka duba lamarin da idon basira su kwayoyin ansan wadanda suke kawo su. Mu a matsayin mu na majalisar matasa idan ka duba bara mun yi wani rangadi da muka wayewa matasa kai a cikin commune ko kananan hukumomi guda biyar dake yankin Gidan Roumdji tare da gudunmowar majalisar shawara na wadannan kananan hukumomi. Yau idan ka lura mu matasamuna cikin wani hali musamman kan abinda ya shafi harkar tsaro da ya lalace a yanzu inda wadanda suka fi shan wahala ciki duk matasa ne  da kuma mata. Kenan mu fafutukar da muke na waye kai ne da kuma kai koke wajen hukumomi don a samar wa wadannan matasa aiki. Wannan shine muka fi yi a matsayinmuna shugabannin matasa a gundumar Gidan Roumdji. »

Tushen wadannan matsaloli suna da alaka kai tsaye ne ga rashin aikin yi da kuma zaman banza ga matasa. Akan haka ne shugaban majalisar matasa na da’irar birnin Maradi da kewaye cewa da Abdourahmane Halidu Issa majalisar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu suke shirya ma matasan horo kan ayyukan hannun da kuma samar musu da gurbin karatu a cikin makarantu don ganin sun kange su daga shiga cikin matsaloli.

« Abinda muka yi musamman a bangaren majalisar matasa ta da’irar birnin Maradi shine tun lokacin da mu ka zo, mun nemi kulla alaka da wasu makarantu masu zaman kansu inda muke dauko matasan da basu da karfin biyan kudaden karatu,ko kuma marayu sai mu biya musu karatu. Muna kaisu makarantun koyon ayyukan hannu don kwarewa, ko kuma mu shirya musu horo na wani dan lokaci don su dogara da kansu ta hanyar horon da suka samu. Idan muka dauka misali a shekarar bara mun horar da matasa 154. Sannan daya daga cikin abinda yake addabar matasa akwai rashin aikin yi, to a dalilin haka mun kulla wata yarjejeniya da wasu makarantun koyon tukin mota inda suka mana ragowar kudaden da ake biya don baiwa matasa damar mallakar lasisin tukin mota sakamakon cewa anan birnin Maradi, matasa na da kokarin tukin adaidaita sahu domin dogaro da kai, inda ta wannan hanya matasan zasu samu damar tuki yadda suke so kuma cikin kwanciyar hankali. »    

A cikin birane kamar na Maradi sanin kowa ne matasa na fama da harkar shaye shaye da kuma shiga harakokin banga. A cewar Abdurahmane Halidu, wannan dalili ne ya sa wani lokaci suke shirya taron wayar da kai ga matasan domin tunatar dasu illar shaye shaye.

« A kowane lokaci muna zama musamman da hukumomi da kuma kwararru wadanda suka san matsalolin shaye shaye. A wani lokacin mun yi zama karamar hukumar da’ira ta biyu inda muka tara matasa muka tattauna bisa kan menene illolin shaye shaye da kuma abinda suke haddasawa a gare su da kuma yadda za su dauki matakin kiyaye shi da kuma hukuncin da zai iya hawa kan mutum idan ya aikata laifin shaye shaye. »

Daga karshe shugaban majalisar matasa na karamar hukumar Gidan Roumji cewa da Yacouba Labo Madugu yayi kira ga matasa don ganin sun samu aiki domin dogaro da kansu da kuma kare kansu daga aikata mummunan ayyuka.

« Kira na karshe da zan yi ga matasa shine mu tashi tsaye. Mu nemi ilmi kuma mu nemi aiki musamman ma aikin hannu saboada mu kawo tamu gudun mowa wajen wanzar da zaman lafiya. Sannan idan mun ga abinda bamu yarda da shi ba, to mu yi kokarin sanar da hukumomi na kusa don a dauki mataki kan wani ko wata su cutar da jama’a idan har mugu ne. »

A bayyane take cewa matasan jahar Maradi sun dukufa wajen ganin sun kawo gudun mowarsu don gyara halayen matasa don ganin basu shiga miyagun ayyuka ba. Da fatan  hakan zai taka mahimmiyar rawa wajen samun rayuwa ta gari ga dimbin matasan da jahar ke da su. 

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )