
Jemage: Muhimman abokan kare muhalli.
« Jemage na cin kwari musamman sauro da kwarin da ke lalata amfanin gona. Wasu nau’ukan kuma suna cin ‘ya’yan itatuwa, ruwan furanni da kuma wasu kananan dabbobi. »
Jemage na daga cikin dabbobin da mutane kan ji tsoro ko rashin yarda da su, musamman saboda yadda suke bayyana da dare. Sai dai duk da wannan ra’ayi, jemage na taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye daidaiton muhalli. Wasu nau’ukan jemage suna cin kwari masu yawa, yayin da wasu ke taimakawa wajen yada iri da kuma fitar da furannin tsirrai. Hakan na da matukar muhimmanci ga muhalli da kuma aikin gona.
Jemage na taimakawa wajen rage yawan kwari masu cutarwa :
Da zarar dare ya fara, jemage kan bar wuraren da suke fakewa domin neman abinci. Suna iya zama a cikin kogo, ramukan bishiyoyi, dazuzzuka, ko kuma wasu gine-gine da ba a amfani da su.
A cewar Abdoul Rachidou Mahaman Salissou, mai bincike kan harkokin kiwon dabbobi a Jami’ar Maradi, wasu nau’ukan jemage suna cin kwari musamman sauro da kwarin da ke lalata amfanin gona.
« Jemage na cin kwari musamman sauro da kwarin da ke lalata amfanin gona. Wasu nau’ukan kuma suna cin ‘ya’yan itatuwa, ruwan furanni da kuma wasu kananan dabbobi. »
Wannan dabi’a ta jemage na taimakawa wajen rage yawan wasu kwari masu cutarwa ga mutane, dabbobi da amfanin gona. Ta haka ne suke taka rawa a matsayin masu taimakawa wajen kare amfanin gona ta hanyar halitta.
Suna taimakawa wajen fitar da furanni da yada iri :
Amfanin jemage bai tsaya kawai kan cin kwari ba. Wasu nau’ukansu da ke cin ‘ya’yan itatuwa da ruwan furanni suna taimakawa wajen yada pollen daga wannan shuka zuwa wata. Wannan na taimakawa wajen hayayyafa da wasu tsirrai.
Haka kuma, « jemage na taimakawa wajen yada irin tsirrai ta hanyar abin da suke ci da kuma yadda suke tafiya daga wani wuri zuwa wani. Wannan na taimakawa wajen farfadowar wasu nau’ukan tsirrai da kuma kare nau’o’in halittu. » a cewar sa. « Bugu a kari, kashin jemage, wanda ake kira guano, na iya taimakawa wajen inganta kasa, saboda yana dauke da sinadarai kamar nitrogen da phosphorus. »
A cewar Abdoul Rachidou Mahaman Salissou, duk da matsalolin da jemage ke fuskanta, suna da muhimmiyar rawa wajen kiyaye daidaiton muhalli da kuma taimakawa aikin gona.
Don haka, wayar da kan jama’a na da muhimmanci wajen kare wadannan dabbobi. Kare bishiyoyi, guje wa lalata wuraren da suke fakewa da kuma kare muhalli na daga cikin matakan da za su taimaka wajen ci gaba da kasancewar jemage.
Sai dai ana bukatar taka-tsantsan. Bai kamata a taba jemage kai tsaye ba, domin cudanya da dabbar da ke dauke da wata cuta na iya haifar da hadarin lafiya.

