
Maradi: Kasuwancin ’ya’yan giggiya na samar da kuɗin shiga ga matasa, amma yana barazana ga itatuwa.
A nan Maradi, kasuwancin ’ya’yan giggiya, wanda wasu ke kira da kwolo, na ci gaba da jan hankalin matasa, musamman ’yan mata da ke gudanar da wannan sana’a domin samun kuɗin shiga. Sai dai, a bayan wannan sana’a akwai wata barazana ga muhalli, sakamakon cire ’ya’yan itatuwa tun ba su nuna ba, lamarin da ke kawo cikas ga sake tsirowar itatuwa. To, mene ne ya sa matasa suka rungumi wannan sana’a, kuma wace illa take haifarwa ga muhalli?
Sana’ar da ke taimaka wa matasa wajen magance zaman banza
A duk safiya, a titunan birnin Maradi, ana ganin wasu ’yan mata dauke da ’ya’yan giggiya a cikin ƙananan ledoji, suna yawo domin sayarwa. Nana Khadija, wadda aka fi sani da Maman Sani, na daga cikin matasan da suka rungumi wannan sana’a domin samun abin dogaro da kai.
Ta bayyana cewa wannan sana’a na taimaka mata wajen samun kuɗin shiga da kuma guje wa zaman banza.
Nana Khadija ta ce:
“Duk safiya ina sayen ’ya’yan giggiya na kuɗi tsakanin CFA 1,500 zuwa 1,750, sannan in sayar. Duk da cewa ciniki yana da yanayi, wani lokaci ana samun ciniki sosai saboda mutane na saye. Ina yin wannan sana’a ne domin magance zaman banza.”
Sana’ar da ke fuskantar wasu ƙalubale
Ba ’yan mata kaɗai ne ke gudanar da wannan sana’a ba, domin akwai matasa maza da ke shigo da ’ya’yan giggiya daga ƙasar Najeriya domin sayarwa a Maradi.
Oumar Farouk, wanda aka fi sani da Auta, ya ce ya shafe shekaru biyar zuwa shida yana wannan sana’a. A cewarsa, sana’ar na taimaka masa wajen samun abin masarufi, duk da wasu matsalolin da yake fuskanta yayin shigo da kayan daga Najeriya.
Oumar Farouk ya bayyana cewa:
“Gaskiya na kai shekaru biyar zuwa shida ina wannan sana’a, kuma ina samun abin rufa wa kai, duk da cewa har yanzu ban gina gida ba. Daga Najeriya nake shigo da ’ya’yan giggiya, sannan in sayar wa ’yan mata. Sai dai muna fuskantar matsaloli wajen shigo da su, inda jami’an kwastam ke tilasta mana auna kayan, duk da takardun da muke samu daga jami’an kula da gandun daji.”
Barazana ga rayuwa da cigaban itatuwa
Duk da cewa wannan sana’a na samar da kuɗin shiga ga matasa, cire ’ya’yan itatuwa tun ba su nuna ba na zama babbar barazana ga muhalli. Hakan na iya hana wasu ’ya’yan itatuwa balaga da kuma rage damar da suke da ita ta sake tsirowa.
Wani jami’in kula da gandun daji a yankin Chadakori ya bayyana illolin wannan dabi’a ga itatuwa.
Jami’in gandun dajin ya ce:
“Wannan babbar matsala ce ga itatuwa, domin ba a barin ’ya’yan su nuna. Hakan na taimakawa wajen bacewar wasu nau’ikan itatuwa daga doron ƙasa. Sai dai, galibi ana fuskantar wannan matsala a lokacin tsanani, lokacin da mutane ba su da isasshen abinci, don haka wasu ke sayar da ’ya’yan domin neman abin da za su ci. Wannan babbar matsala ce, shi ya sa muke ci gaba da wayar da kan jama’a game da illar cire ’ya’yan giggiya ko goriba tun ba su nuna ba.”
Baya ga ’ya’yan giggiya, akwai wasu nau’ikan itatuwa da su ma ke fuskantar irin wannan matsala. Idan aka ci gaba da cire ’ya’yansu kafin su nuna, hakan na iya rage yawaitar itatuwa, raunana ciyayi da kuma ƙara haɗarin zaizayar ƙasa.
Saboda haka, akwai buƙatar wayar da kan masu wannan sana’a da sauran al’umma kan muhimmancin barin ’ya’yan itatuwa su nuna kafin girbewa, domin a daidaita neman abin masarufi da kuma kare muhalli.
Kare itatuwa a yau na nufin samar da ingantaccen muhalli da kuma albarkatun da za su amfani al’ummomi a nan gaba.
Illia Moumouni.

