Darakta Janar na Cibiyar Caima na ziyarar wuraren ajiyar takin zamani abincin dabbobi da kayan noma a Maradi

Darakta Janar na Cibiyar Caima na ziyarar wuraren ajiyar takin zamani abincin dabbobi da kayan noma a Maradi

Dakta Isufu Bawa na ziyarar ne don gani da ido yanayin saida takin na zamani da abincin dabbobi da sauran kayan noma da gwamnati ta ware wa manoman Jihar Maradi.Wannan ziyara dai ta shafi suto suto ne na ajiyar takin na zamani da kayan noma.

Gamsuwa da yadda aka siyar da takin zamani

Dakta Bawa ya bayyana farin cikinsa yana mai cewa « Na ji dadin yadda manoma da makiyaya a Jihar Maradi suka samu takin zamani, abincin dabbobi  da kayan noman da aka ware musu daidai da bukatunsu ».

Jihar Maradi ta kasance ta biyu a Nijar wajan samun takin zamani kala kala da sauran kayan noma inda ta samu ton dubu 5.445.5. wannan ya shafi taki sanfarin PRSA, da  DAP, sai  NPK da kuma  l’Urée ; Takin zamnin na Caima tallafi ne na kasar Rasha. Takin da Jihar Maradi ta samu na zama kashi 14 cikin 100 na yawan takin da kasar Nijar ta samu gaba daya kusan ton 38.880,8.

Daga cikin ton dubu 5.445,5 da Jihar Maradi ta samu ya zuwa yanzu abin da ya rage bai wuce ton 511, 65, kusan kashi 90.6 cikin dari na takin an siyar da shi ga manoma.

Caima yanzu bayan siyar da takin zamani  ga manoma ta kara da abincin dabbobi. Wannan canjin dai a cewar Darakta Janar na Caima, bukata ce daga shugaban kasa Janar Abdourahamane Tiani ta hanyar wani kudurin da ya dauka mai lamba 20-25 na 03 ga watan Faburairu 2025 da ya karawa Caima fagen aikinta, bayan takin zamani da kayan noma aka kara mata yanzu da abincin dabbobi.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )