
Cututtukan zuciya: Kyawawan halaye na taimakawa wajen kare lafiyar zuciya.
« Shan taba sigari na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen haifar da cututtukan zuciya. Don haka bai kamata a sha taba ba, kuma musamman bai kamata a sha barasa ba. »
A yayin bikin ranar zuciya ta duniya 29 gawatan satumba, ana jaddada muhimmancin yin rigakafi da kuma kiyaye lafiyar zuciya. Cututtukan zuciya na daga cikin manyan matsalolin da ke barazana ga lafiyar al’umma. Sai dai masana sun bayyana cewa, ana iya rage wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa waɗannan cututtuka ta hanyar bin kyawawan halaye na rayuwa.
Motsa jiki da ingantaccen abinci na taimakawa wajen kare zuciya :
Rigakafin cututtukan zuciya ya dogara ne da sarrafa abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da su. A cewar Dakta Fataou Chaibou, likita a Asibitin Kwararru na Maradi, yin motsa jiki a kai a kai na daga cikin muhimman matakan kariya.
« Manyan halayen da ya kamata a bi domin kare kai daga cututtukan zuciya su ne waɗanda galibi muke sakaci da su. Da farko akwai motsa jiki. Wannan wata muhimmiyar hanya ce wajen rage cututtukan zuciya » in ji shi.
Likitan ya ba da shawarar yin motsa jiki na tsawon mintuna 150 zuwa 200 a cikin mako guda, wato kusan sau biyu zuwa uku a mako, na tsawon mintuna 30 zuwa 40 a kowane lokaci.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin cin abinci mai gina jiki da kare lafiya. Ya shawarci rage cin kitse, musamman kitse mai nauyi, da yawaita cin ’ya’yan itatuwa da kayan lambu. Haka kuma, ya kamata a rage yawan sukari, gishiri da kuma abubuwan sha masu ɗauke da sukari.
Kula da nauyin jiki da guje wa taba sigari da barasa :
Kula da nauyin jiki yana daga cikin muhimman matakan kare lafiyar zuciya. Yin kiba fiye da kima na iya ƙara haɗarin samun wasu matsalolin da suka shafi zuciya da jijiyoyin jini.
Dakta Fataou Chaibou ya ce:
« Ya kamata a kiyaye nauyin jiki mai kyau. Idan mutum yana da kiba, ya kamata ya rage ta kuma ya guji ƙara nauyi. »
Ya kuma yi gargadi game da illar taba sigari da barasa, yana mai cewa shan taba na daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya.
« Shan taba sigari na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen haifar da cututtukan zuciya. Don haka bai kamata a sha taba ba, kuma musamman bai kamata a sha barasa ba. » a cewar sa .
Saboda haka, cin abinci mai kyau, yin motsa jiki akai-akai da kuma kula da abubuwan da ke ƙara haɗarin cututtukan zuciya na daga cikin muhimman matakan kare lafiyar zuciya. Kyawawan halaye da mutum ya riƙa aikatawa a kullum na iya taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da waɗannan cututtuka.

