lokacin damina: Cututtukan numfashi na barazana ga yara.

lokacin damina: Cututtukan numfashi na barazana ga yara.

« A yanayin yankin Sahel da muke ciki, inda yanayin zafi ke raguwa, sannan danshi ke karuwa, cututtukan numfashi sun fi yawaita tsakanin yara. Ana samun cutar mura ta hanci da makogaro, mashako, ciwon makogaro, sannan a wasu lokuta masu tsanani, ana iya samun ciwon huhu.»

A lokacin damina, yara, musamman wadanda garkuwar jikinsu ba ta da karfi sosai, na cikin wadanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan numfashi. A yankunan Sahel, sauyin yanayin zafi, danshi, cunkoson jama’a da kuma hayakin da ake samu a gidaje na iya taimakawa wajen bullar wadannan cututtuka ko kara tsananta su. Wasu daga cikin cututtukan numfashi na iya zama masu tsanani ga kananan yara, musamman idan suka rikide zuwa ciwon huhu.

A cewar Dokta Mahaman Daha Daouda Ali, kwararre kan nazarin lafiyar jama’a, fasahar zamani da kirkire-kirkire, cututtukan numfashi sun fi yawaita ga yara a wannan lokaci.

« A yanayin yankin Sahel da muke ciki, inda yanayin zafi ke raguwa, sannan danshi ke karuwa, cututtukan numfashi sun fi yawaita tsakanin yara. Ana samun cutar mura ta hanci da makogaro, mashako, ciwon makogaro, sannan a wasu lokuta masu tsanani, ana iya samun ciwon huhu.» a cewar sa.

A cewar kwararre kan nazarin lafiyar jama’a, mafi yawan wadannan cututtuka na samun asali ne daga kwayoyin cuta na virus, kodayake wasu na iya samo asali daga kwayoyin bacteria. Wasu abubuwa kuma na iya kara tsananta halin lafiyar yara, ciki har da cunkoson jama’a, yawan zama cikin iska mai sanyi, hayakin itace ko gawayi, da kuma rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki.

Wasu cututtukan numfashi da virus ke haddasawa, musamman wadanda ke da alaka da Respiratory Syncytial Virus (RSV), na iya haifar da mummunar rashin lafiya ga kananan yara.

Matakai masu sauki na kare kananan yara :

A wannan yanayi, kariya na da matukar muhimmanci. Dokta Mahaman Daha Daouda Ali ya shawarci iyaye da su kare yara daga sanyi, tare da guje wa barin su cikin iska mai danshi ko sanyi na tsawon lokaci, musamman da safe da kuma lokacin faduwar rana. Ya kuma jaddada muhimmancin tsaftace muhallin gida. Wannan ya hada da bude tagogi domin samun iska mai kyau, amma ba tare da barin iska mai karfi ta rika bugawa yaro kai tsaye ba. Haka kuma, ya kamata a rage hayakin itace ko gawayi a wuraren da yara ke zama ko kwana.

«Wanke hannu da kyau yana da matukar muhimmanci, saboda kwayoyin virus da dama suna yaduwa ta hanyar mu’amala. Haka kuma, yana da muhimmanci a samar wa yara abinci mai kyau domin karfafa garkuwar jikinsu, sannan a gaggauta kai su cibiyar lafiya da zarar an fara ganin alamun rashin lafiya.»

Lokacin damina na bukatar iyaye su kara taka-tsantsan wajen kula da lafiyar yara. Ko da yake ba zai yiwu a kawar da danshi da sauyin yanayin zafi gaba daya ba, matakai masu sauki a gida na iya taimakawa wajen rage hadarin kamuwa da cututtuka. Idan yaro ya fara nuna alamun rashin lafiyar nunfashi, yana da muhimmanci a gaggauta kai shi cibiyar lafiya domin samun kulawar da ta dace kamin cutar ta koma cutar asthma.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )