Babbar Kasuwar Maradi: Bayan shekaru 11, har yanzu ana fuskantar kalubalen bashi da rashin samun cikakken kudin shiga

Babbar Kasuwar Maradi: Bayan shekaru 11, har yanzu ana fuskantar kalubalen bashi da rashin samun cikakken kudin shiga

Maradi: Bayan shafe shekaru 11 da fara aikin gina da gudanar da babbar kasuwar birnin Maradi, har yanzu kasuwar na fuskantar manyan kalubale da suka shafi bashin da aka ciwo domin gina ta, da kuma rashin samun kudaden shiga yadda ya kamata.

 

Wannan yanayi ya sa wasu daga cikin masu zuba jari a kasuwar suka fara nuna damuwa, yayin da ake ci gaba da kokarin nemo hanyoyin da za a farfado da harkokin kasuwar tare da tabbatar da cewa masu hannun jari sun fara cin moriyar jarin da suka sanya.

 

Babbar Kasuwar Maradi na daga cikin manyan kasuwannin zamani da aka gina a Nijar. Yayin da gwamnati ta dauki nauyin gina wasu manyan kasuwanni, irin su na Zinder da Tahoua, gina babbar kasuwar Maradi ya samu hadin gwiwar ‘yan kasuwa, Ma’aikatar Da’irar Birnin Maradi da kuma gwamnati.

Sai dai, bambancin tsarin samar da kudin gina kasuwar ya sa aka ciwo bashi, lamarin da ya kasance daya daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye harkokin kasuwar.

Kudin haya da kuma kokarin jawo ‘yan kasuwa

A cewar babban daraktan babbar kasuwar Maradi, Alhaji Sadda Sani Gwanda, « hukumar kasuwar ta yi kokarin rage kudaden shaguna domin jawo ‘yan kasuwa da kuma bunkasa harkokin kasuwar.

 duk da cewa ana yawan sukar yadda kasuwar ba ta samar da sakamakon da ake bukata ba, ba za a iya kwatanta kudin shagunan kasuwar da na wasu wurare ba.

 A wasu shagunan da ke kusa da tashar motoci a Maradi, ana iya samun haya har zuwa  (60,000f), yayin da a babbar kasuwar Maradi ake bayar da shago kan (15,000f).

Saboda haka, hukumar ta gudanar da nazari kan halin da ake ciki, inda ta yanke shawarar kara (5,000f) kacal a kan kudin haya na kowane shago, maimakon yin karin kudi mai yawa.

Burin hukumar shi ne a ci gaba da inganta harkokin kasuwar a hankali, har zuwa lokacin da za a iya samun riba da kuma rabawa masu hannun jari. »

Bashin BSIC na kusa da kawo karshe

A nasa bangaren, shugaban masu zuba hannun jari a harkar babbar kasuwar Maradi, Alhaji Sabiou Musa Kalla, «  akwai alamun cewa ana samun ci gaba wajen warware matsalolin da suka dabaibaye kasuwar. Saboda akwai bashin da ke tsakanin babbar kasuwar Maradi da bankin BSIC, wanda ya kai kimanin  biliyan 3,3 na kudin CFA , mu jagororin mun hannun jari sun matsa wa gwamnati lamba domin ta dauki nauyin wannan bashi, kuma an samu ci gaba wajen biyan bashin.

Adadin kudin da ya rage gwamnati ta biya ya kai kimanin  miliyan 500 na CFA. »

Shaguna 88 da ba a kammala ba

Baya ga batun bashi, akwai kuma shaguna kimanin 88 da dan kwangilar da aka ba aikin bai kammala ba  a cewar Alhaji Sabi’u Musa Kalla.

« wannan batu ma na dab da zuwa karshe, sakamakon matsin lamba da dagewar da masu ruwa da tsaki suka yi wajen ganin an kammala aikin.

Haka kuma, matsalar gobarar da ta afku a babbar kasuwar a watan Fabrairun 2026 na daga cikin batutuwan da ake kokarin warwarewa.

tunda kamfanin inshora ya turo wakilinsa domin gudanar da bincike kan gobarar, kuma yanzu abin da ya rage shi ne a fitar da kudin da za a yi amfani da shi wajen gyara shagunan da gobarar ta lalata.

Don haka tune an fara shirye-shiryen nemo ‘yan kwangilar da za su gudanar da aikin gyaran shagunan da suka kone. »

Me ke gaba?

Yayin da wasu daga cikin matsalolin babbar kasuwar Maradi ke samun hanyar warwarewa, abin jira shi ne yadda hukumar kasuwar, masu hannun jari da gwamnati za su ci gaba da aiki tare wajen farfado da harkokin kasuwar.

Haka kuma, ana sa ran cewa warware matsalar bashin, kammala shagunan da ba a gama ba, da gyaran wuraren da gobara ta lalata, za su taimaka wajen kara kudaden shiga da inganta yanayin gudanar da kasuwar.

Idan aka samu nasarar shawo kan wadannan matsaloli, masu hannun jari na fatan ganin babbar Kasuwar Maradi ta fara samun riba, tare da samun damar raba ribar ga masu hannun jarin da suka sanya jari tun daga farko.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )