Maradi: Cin zarafin mata a gidajen aure na ci gaba da zama babban kalubale

Maradi: Cin zarafin mata a gidajen aure na ci gaba da zama babban kalubale

Cin zarafin mata a cikin gidajen aure na ci gaba da zama wani babban kalubale a cikin al’umma. Daga duka da wulakanci zuwa hana mata ‘yancin gudanar da harkokinsu na yau da kullum, wasu matan aure na fuskantar matsaloli da dama a hannun mazajensu. Wannan lamari na jefa su cikin damuwa da kunci, tare da kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin iyali.

 

Wasu mata na rayuwa cikin tsananin kunci

A birnin Maradi, wasu matan aure na fuskantar cin zarafi iri-iri a cikin gidajensu. Wata mata da ta fuskanci wannan matsala ta bayyana irin halin da take ciki, inda ta ce mijinta na dukan ta a gaban ‘yarta, tare da hana ta gudanar da duk wata sana’a da za ta taimaka mata wajen dogaro da kanta.

Ta ce:

« Yanzu halin da nake ciki a gidan aurena akwai damuwa sosai. Idan mijina ya fusata, yakan doke ni har a gaban ‘yata. Haka kuma yana hana ni yin duk wani abu da zan iya taimaka wa rayuwata, kamar karamar sana’a ko wani aiki makamancin haka. Har ma da zuwa makarantar karatun addini na, ya hana ni. »

Gidan Alkali na daga cikin wuraren neman taimako

Dangane da wannan matsala, wasu mata na komawa ga hukumomi da cibiyoyin da ke da alhakin kare hakkokinsu domin neman mafita daga halin da suke ciki.

A Maradi, gidan Alkali na daga cikin wuraren da mata ke kai koken matsalolin da suke fuskanta a gidajen aurensu. Alkali Ousmane ya bayyana cewa suna karbar koke-koken mata, musamman wadanda suka shafi duka da sauran nau’o’in cin zarafi.

A cewarsa, suna kokarin sasanta tsakanin ma’auratan tare da jan hankalin mazajen da ake zargi da cin zarafi. Idan kuma matsalar ta ci gaba, sai su tura wadanda abin ya shafa zuwa sauran hukumomin da suka dace, kamar Jandarma da sauran cibiyoyin kare hakkin mata.

Talauci da rashin sanin doka na cikin abubuwan da ke haddasa matsalar

A nasa bangaren, Abdou Issa, daya daga cikin masu fafutukar kare hakkin dan Adam, ya bayyana cewa talauci da rashin sanin dokokin da ke kare mata na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen yawaitar cin zarafi a gidajen aure.

Ya ce, dogaro da miji gaba daya wajen biyan bukatun yau da kullum na iya haifar da raini da wulakanci a wasu gidajen aure, musamman idan matar ba ta da sana’ar dogaro da kanta.

Ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan al’umma, musamman maza, game da dokokin da suka shafi kare mata, domin su fahimci cewa cin zarafin mata laifi ne kuma yana iya janyo hukunci.

Duk da kokarin da kungiyoyi da hukumomi ke yi wajen wayar da kan al’umma, cin zarafin mata a gidajen aure na ci gaba da kasancewa abin damuwa. Hakan na nuna bukatar kara karfafa wayar da kai, kare hakkokin mata da kuma samar da zaman lafiya da mutunta juna tsakanin ma’aurata.

Rahoto: Illia Moumouni

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )