
Motuna masu caji na ya yi a Maradi saboda matsalar isansi
tsadar man fetur dai ta sa kadan kadan wadannan motuna na kara yawa tsakanin al’ummar Maradi saboda irin lokacin da ake batawa wajan neman isansi a gidajen mai, Malam Mahamadu na ciki wadanda suka jingine motunansu masu aiki da isansi.
Moto mai aiki da wutar lantarki ba kara, ba shan essense ga zirga zirga har ta kilometa 50 zuwa 70, tsadar man fetur dai ta sa kadan kadan wadannan motuna na kara yawa tsakanin al’ummar Maradi saboda irin lokacin da ake batawa wajan neman isansi a gidajen mai, Malam Mahamadu na ciki wadanda suka jingine motunansu masu aiki da isansi.
« Tun da ni mai isansin ma ke gareni, wajan jika dari bakwai ma na siyeshi, da naga yanayin yadda abubuwa suke kawai na ba kaina lafiya, nace a kawo mani mai aiki da caji, don ni yanzu gaskiya saboda Allah in naga mutum station yana tsaye yana jiran mai, wallahi har tausayi yake bani, sai inje cikin gari in yi uzurina in dawo in tarda mutum yana nan tsaye yana jiran. Don ni yanzu kudin da ni ke kashewa ga wancan mai mai, sune na maida kudin wutar lantarki ta gidana da ruwa kai har da Gas na dahuwa. »
Ibrahim Garba ya kan aje motarsa wasu lokutan idan man ya yi wahala ya bayyana alfanon da ya gani ga moton mai aiki da wutar lantarki ko electrique.
« A gaskiya a karshe dai na aje mota da moto nike zirganiyata mai caji, baya da shan wuta in aka kwatanta ga isansi, ga moto karamci ace mutum kullum ka sha lita daya, kun ga wata jika sha biyar kenan, shi kuma wanga a wuni bai wuce ya sha kilowat biyu ba in ka sa caji, kenan kilowat biyu dala arba’in,mota karamci mutum ya sha lita biyar a wuni, kun ga a wata karamci mutum zai sha man jika sittin, saba’in zuwa tamanin a wata, gaskiya sauki sosai sosaima da sosai »
Kakar wasu dai ta yanke saka irinsu Okashatu dake siyar da irin wadannan mashinan, yace bukatar sai karuwa take
«Kwanan nan mun siyar da wani jika dari biyu da ishirin, amman duk wanda ya yi magana ana kawo masa har na dari hudu, har na dari uku ana samu, da muna siyar da hudu a wata amma yanzu yana kai goma, akwai na dari hudu na dari uku har na dari biyar ana samu, har na dari biyar da hamsin ana samu gaskiya. »
Watanni kusan 5 da wannan matsalar karamcin man ta fara ana iya cewa dai Maza da mata yara da manya a wannan gari na maradi sun samu hanyar magance wannan matsala ta karamcin isansi ta hanyar amfani da motuna masu aiki da wutar lantarki.

