Maradi : Matasa na ƙara himma wajen kare muhalli.

Maradi : Matasa na ƙara himma wajen kare muhalli.

« Muna gudanar da zaman wayar da kan jama’a kan muhalli, musamman yadda za a kare albarkatun ƙasa da kuma muhimmancin tsaftar muhalli. Muna kuma ƙarfafa matasa da su fahimci cewa kare muhalli nauyin kowa ne »,

A garin Maradi, matasa na ƙara taka rawa wajen kare muhalli. Ta hanyar kungiyoyi da ƙungiyoyin matasa, ana gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a, tsaftar muhalli, sarrafa tarkace da kuma dasa bishiyoyi. Waɗannan ayyuka na nuna yadda matasa ke ƙoƙarin bayar da gudunmawarsu wajen magance matsalolin muhalli da ke fuskantar birnin.

Wayar da kan jama’a kan kare muhalli :

Boubacar Abdoul Karim, shugaban Majalisar Matasa ta Yankin Maradi, ya bayyana cewa wayar da kan jama’a na daga cikin manyan ayyukan da matasan ke gudanarwa domin kare muhalli. « Muna gudanar da zaman wayar da kan jama’a kan muhalli, musamman yadda za a kare albarkatun ƙasa da kuma muhimmancin tsaftar muhalli. Muna kuma ƙarfafa matasa da su fahimci cewa kare muhalli nauyin kowa ne », in ji Boubacar Abdoul Karim.

Ya ƙara da cewa wannan wayar da kan jama’a na da nufin sauya ɗabi’un jama’a, musamman wajen zubar da shara da kuma kula da wuraren da suke rayuwa. « Muna son mutane su fahimci cewa ba gwamnati kaɗai ce ke da alhakin tsaftace muhalli ba. Kowanne mutum yana da rawar da zai taka, musamman matasa », ya bayyana.

Daga shara zuwa kayan amfani :

A nasa ɓangaren, Hadi Yahaya, shugaban Club Optimal pour le Développement des Jeunes, COP-J Maradi, ya bayyana cewa ƙungiyarsu ta mayar da hankali wajen neman mafita ga matsalar tarkacen gidaje. « Muna aiki ne wajen sarrafa tarkacen gidaje, musamman buhunan leda. Muna tattara su sannan mu sarrafa su domin mayar da su wasu abubuwan da za a iya amfani da su », in ji Hadi Yahaya.

Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin hanyoyin da suke amfani da su ita ce sauya buhunan leda zuwa pavé, wato duwatsun da ake shimfiɗa a tituna da wuraren zama.

« Muna mayar da buhunan leda zuwa pavé. Wannan yana taimakawa wajen rage yawan buhunan da ke yawo a muhalli, sannan muna kuma samar da wani abu mai amfani daga cikin abin da ake kira shara », ya ƙara da cewa.

A cewarsa, wannan aiki na iya zama wata hanya ta ƙarfafa matasa su shiga harkokin kare muhalli tare da samar da hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Dasa bishiyoyi da kula da su :

A nasa ɓangaren kuma, Saley Moussa Mahaman Issaka, mamba a Initiative pour l’Arbre, ya ce ƙungiyarsu na mai da hankali kan dasa bishiyoyi da kuma kula da su bayan an dasa su. « Ayyukanmu sun fi karkata ne kan dasa bishiyoyi da kuma kula da su. Mun fahimci cewa dasa bishiya kaɗai bai isa ba, dole ne a ci gaba da kula da ita har sai ta girma », in ji Saley Moussa Mahaman Issaka.

Ya ƙara da cewa matasa na da muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan bishiyoyi da kare muhalli. « Muna ƙarfafa matasa da su fahimci muhimmancin bishiyoyi. Bishiya na taimakawa wajen kare muhalli, samar da inuwa da kuma inganta yanayin rayuwa. Saboda haka, bayan dasa bishiya, wajibi ne mu kula da ita », ya bayyana.

Wannan yunƙuri na matasa na iya taimakawa wajen inganta tsaftar birnin Maradi, rage gurɓatar muhalli da kuma ƙara wayar da kan jama’a game da muhimmancin kare albarkatun ƙasa.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )