
Sana’ar gyaran jiki da kwalliya na ƙara samun karɓuwa a birnin Maradi.
Zan bude sashen kula da Amare da matan da suka haihu don gyara musu jiki su koma kamar zinare
Mata da dama ne dai ke dogaro da ita wajen samun abin yi da kuma dogaro da kansu. Daga cikin waɗannan matan, akwai Furayya Muhammad, uwa mai ‘ya’ya biyar, wadda ta shafe sama da shekaru 18 tana wannan sana’a, duk da irin ƙalubalen da ta fuskanta har yau tana ci gaba da sana’arta.
Yar asalin Maradi, Furayya Muhammad, ƙwararriyar mai sana’ar gyaran jiki da kwalliya ce, wadda ta fara koyon sana’ar a Kano a Najeriya, inda take zaune tare da mai gidanta da ‘ya’yansu biyar. A wurinta, wannan sana’a ba kawai hanyar samun kuɗi ba ce, illa wata baiwa ce da ta gada tun daga kakanninta. Bayan ta kware a wannan sana’a, Furayya ta kuma mayar da hankali wajen koyar da wasu matan domin su samu sana’ar da za ta ba su damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki
“Da wannan sana’ar,mu kamar gado ne saboda duk wanda ya taso gidan mu,to yana da bukatar yin harakar magani to yakan iya yi ko maza ko mata.Musamman su maza suna harakar maganin karfe,amma dai mu mata sai muka zabi harakoki wanda ya shafi magungunan mata ne,sirrin ka itace .Mun gada ne tun daga kan kakanni.”
Furayya na amfani da ƙwarewarta wajen samar da kayayyakin da take amfani da su wajen kula da kwastomominta. Abin da ya bambanta sana’arta shi ne yadda take sarrafa wasu daga cikin kayayyakin da kanta, ta hanyar amfani da tsirrai da sauran kayan halitta.
“Ni bana siyo magani a kasuwa don in siyar da shi.Duk maganin da na siyar to ni na sarrafa shi da hannuna kamar su gumba shinkafa,tukudi,gumbar madara,tsumi ,zuma ta mata,zuma ta kiba Kenan da garin sabaya yana dauke da itatutuwa daban daban wadanda suma sukan haddasa kumburin kashi zuwa tsoka.Sai mutun aga yayi kiba Kenan.”
Baya ga kayayyakin kula da jiki da lafiyar mata, Furayya tana yin wasu kayayyakin kwalliya na asali da ake amfani da su wajen kula da fata da gashi. A cewarta, amfani da kaya na gida na daga cikin abubuwan da take ba muhimmanci wajen gudanar da sana’arta.
“Ina sarrafa man gashi wanda zai baiwa mace gashi yayi baki yayi tsayi, ya kashe mata amosannin kai.Sannan kuma ina saida sabulu shima na hadin Musulunci Wanda muke hadashi da hade haden sabululluka kala daban daban wandanda suke gyara fata da wandanda suke dauke da wasu sinadarai da zasu iya kashe mana duk kwayoyin cuta na jikin fata, kamar su kyazbi , kuraje haka da duk wasu tambura tambura, wadanda basu wuce su goge ba. Akwai mai wanda in kayi wanka da shi da wannan sabulunsa na hadin da muka yi,zaka iya shafa wannan man zai baiwa fatarka haske da wani sheik da laushi. Masha’Allah tayi kyau ta kwanta musamman ma abinda ya shafi fuska.”
Sai dai kamar yadda ake samu a kowace sana’a, tafiyar Furayya ba ta rasa ƙalubale ba. Daga cikin matsalolin da take fuskanta akwai ba wa wasu kwastomomi kayayyaki ko hidima a bashi, wanda a wasu lokutan ba sa dawowa su biya . Duk da wannan ƙalubale, Furayya na cewa sana’ar ta samu babban ci gaba idan aka kwatanta da lokacin da ta fara, lamarin da ya sa take gode wa Allah.
“A jihar Kano inda nike zaune ,cikin yardar Allah anan naje nayi register ta gwanmati . Register wadda ta shafi harakar maganin gargajiya, sun bani dama zan iya buda kamar islamique kyames, da na samu wannan damar shine sai na gyara wuri na bude shaon magani.Ai kinga damar da aka samu ai ta ci gaba ce cikin yardar Allahu sakamakon kana dan zubawa a jaka ka fita da shi,ana dan shigowa gida ana siyen daya biyu.har ya kasance kuma yanzu kazo ka bude shago kuma cikn yardar Allahu anci gaba idan an siya,anyi anfani da shi ana ganin anfanin sa.kuma ya kasance yanzu harakar ta Kano na dora wasu akai wadanda yara na ne,suke ci gaba da gudanar da harakokin a can,ni kuma sai nazo na bude reshen shi a asalin kasata Kenan Nijar nan Maradi sakamakon nan ma ina so in fadada abun saboda a ci gaba da yardar Allahu.”
Labarin Furayya Muhammad ya nuna yadda sana’ar gyaran jiki da kwalliya za ta iya zama wata hanya ta samun abin dogaro da kai da kuma ƙarfafa mata wajen samun kudaden shiga.Duk da ƙalubalen da take fuskanta, Furayya na ci gaba da faɗaɗa sana’arta. A halin yanzu, tana shirin samar da wani tsari na musamman na kula da jiki da kwalliya ga sabbin amare da kuma mata da suka haihu. Manufarta ita ce taimaka wa waɗannan mata su samu damar kula da kansu da kuma jin daɗin rayuwarsu. Tafiyar Furayya na iya zama abin koyi ga sauran mata, musamman masu sha’awar sana’a, idan aka haɗa ta da jajircewa da ƙwarewa, za ta iya zama babbar hanyar samun dogaro da kai.

