
Yadda noman kankana ke bunkasa a jihar Maradi
Kasar Maradi na zama daya daga cikin yankunan da ake gudanar da noman kayan cimaka sosai a Nijar, daga ciki har da kankana, dake ci gaba da zama abun neman kudi wajan al’ummar birni da karkara.
Yadda mutane suka gano muhimmancin Kankana a cikin gina lafiyar jikin dan Adam
Kasar Maradi na zama daya daga cikin yankunan da ake gudanar da noman kayan cimaka sosai a Nijar, daga ciki har da kankana, dake ci gaba da zama abun neman kudi wajan al’ummar birni da karkara.
Sakamakon yadda mutane suka gano muhimmancin Kankana a cikin gina lafiyar jikin dan Adam. Sannu a hankali dai noman kankana na samun karbuwa a jihar Maradi, duk da cewa a can baya ba ko ina ake noma ta ba, Umaru Musa da aka fi sani da Umara wani dake shirin noman ta saboda tunkarar watan Azumi yana mai cewa.
«Darajar da Allah yasa kankana tayi shi yasa na ce bana sai na noma ta, a lokacin shigowar azumi, saboda duk in wannan lokacin yazo tun muna shan wahala sosai, kuma tana yankewa, saboda haka da ina noma eka biyu amma bana zan noma biyar, noman ta ba wani abu mai wahala bane, domin cikin kwanaki arba’in kana dibar ta, domin ta zama cimaka a yanzu, don haka idan Allah yasa ka shibka kankana to duk inda hankalinka yake yana dawo ne gare ta, tana son kula sosai.ba zai yiwu ka naman ta tsaya cikin gari kana fagamaniya, domin kullum tana son a diba ta, shike sa kaga tayi kwari tayi kyau ta na baiwa mutanenmu shawa sosai»
A can baya dai masu noman kankanar na saka ta bayan daukewar ruwan sama, abin da ke sa wani lokaci ta na karamcin a cikin jihar, hakan yasa Alhaji Sani Babbar Giwa daya daga cikin mutanen farko da suka fara nomanta a cikin Damina ga abinda yake cewa.
« Ina iya cewa ni na fara kawo noman kankana a nan Maradi, dan a lokacin da na shibka ta yammacin gada, har mutane na cewa ma wahalar banza ce nike, to cikin hukuncin Allah sai tayi kyau, hakan yasa mutane suka bukaci in gwada musu yadda ake noman ta, a yanzu cikin hatsi sata ake tun da tafi saka wake, domin mai kankana sai ya yi girbi mai sa gujiya bai yi ba, idan mutun zai shuka kankana yar Damina to ya yi biznen ta, in har ta fito ba bu abin da abin da zai sameta ko da an dauke ruwa na dogon lokaci, ita kankana ko Aya ba tayi shan taki ba.»
To duk da hakan lokacin Azumin ramadan an fi bukatar ta, abin da ke haddasa yankewar ta, hakan yasa Umara ya nuna bukatar cewa kowa yakama noman ta.
« Kalubalen da muke samu idan aka noma ta nan cikin gida sai a samata tsada, sai ka ga wadda ake shigowa da ita daga waje tafi sauki, wannan abin daga rashin yawan manoman ta ne, Allah ya sa mutanenmu su gane muna iya yin kawo wadatarta, saboda muna da kasar noman da zamu iya noma wadatatta har ta ishi Maradi baki daya.»
Itama dai kankana kamar sauran kayan gona take wajan bukatar taki, duk da yake tana da hakurin rashin ruwa.

