Tsadar man fetur na ƙara wa malaman makarantun boko wahalar komawa aiki a Maradi.

Tsadar man fetur na ƙara wa malaman makarantun boko wahalar komawa aiki a Maradi.

Yayin da sabuwar shekarar karatun 2026-2027 ta fara, tsadar man fetur na ci gaba da jefa malaman makarantun boko a jihar Maradi cikin ƙarin kuɗaɗen zirga-zirga. Matsalar ta fi shafar malaman da ke aiki a yankunan karkara, musamman wuraren da ake fama da ƙarancin gidajen mai.

 

A Tessaoua, malamin makaranta Mahamane Ali Saïdou ya ce, duk da cewa akwai gidajen mai da dama, dogayen layukan da ake samu a gidajen man na tilasta musu neman mafita a kasuwar bayan fage domin samun damar zuwa wuraren aikinsu.

“A wasu lokuta muna tilastawa kanmu sayen fetur a kasuwar bayan fage domin mu samu damar zuwa wuraren aikinmu. Amma idan man fetur ya samu sosai, muna bin dogayen layuka domin sayensa kai tsaye daga gidan mai.”

Tsadar fetur na ƙara nauyin zirga-zirga

A yankin Kornaka kuwa, Tinta Souley na fuskantar irin wannan matsalar wajen zuwa wurin aikinta, wanda ke da nisan kusan kilomita takwas daga gidanta. A cewarta, farashin fetur ya yi matuƙar tashi idan aka kwatanta da na baya.

Ta ce tsadar man fetur na shafar kudin safarar jama’a, musamman a wuraren da hanyoyin ba su da kyau, inda farashin mota zai iya ƙaruwa gwargwadon yanayin hanya da nisan tafiya.

Shi ma Ibrahim Moumouni Abdou, malamin makaranta da ke aiki a Kornaka 2, ya ce tsadar fetur na sa malamai masu zirga-zirga tsakanin gida da wurin aiki kashe kuɗi mai yawa.

Ya bayyana cewa yana amfani da kusan lita biyar na fetur wajen zuwa da dawowa daga wurin aikinsa. Idan aka yi la’akari da cewa ana sayar da lita ɗaya tsakanin CFA 1,100 zuwa 1,150, kudin zirga-zirgar yau da kullum na zama babban nauyi a gare shi.

Kungiyar malamai ta nemi gwamnati ta ɗauki mataki

Matsalar tsadar man fetur ta kuma jawo hankalin ƙungiyoyin malaman makarantun boko. Magatakardar ƙungiyar SYNACEB reshen jihar Maradi, Farsanté Magaji, ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da za su sauƙaƙa wa malamai da sauran jama’a samun fetur a farashi mai sauƙi.

A cewarsa, farashin litar fetur a kasuwar bayan fage a yanzu yana tsakanin CFA 700 zuwa 1,500, lamarin da ke ƙara tsananta matsalolin rayuwa da na zirga-zirga.

Ya ce ya kamata a samar da hanyoyin da za su tabbatar da cewa fetur yana samuwa a gidajen mai, tare da rage dogaro da kasuwar bayan fage. Ya kuma yi kira da a samar da farashin da zai fi sauƙi ga jama’a.

Ga malaman makarantun boko, musamman waɗanda ke aiki a yankunan da ke da nisa daga gidajensu, samun man fetur a farashi mai sauƙi na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen sauƙaƙa musu komawa da ci gaba da gudanar da ayyukan koyarwa a sabuwar shekarar karatu ta 2026-2027.

Illi Moumouni.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )