Muhimmancin adana resit na shaidar siyayya kaya

Muhimmancin adana resit na shaidar siyayya kaya

Rashin amsar shaidar siyan kaya ko aikewa da kudi cewa da resit wani abu ne dake kara yawa tsakanin al’umma duk da muhimmancinsa wajan rigakafin rigingimun kudi ko musayar kaya.

Wannan kuma na zama babbar matsala wasu lokutan idan wata rigima ta taso. Mutane da dama dai na fadawa cakwakiya saboda rashin resit, Malam Auwalu Yakuba na cikin wadanda ba sa amsar resit inda yake cewa“A’a ni gaskiya ba na adana risit na shaidar siyayya saboda an riga an bani kayana don haka bay a  da wani amfani koda ka aje shi ka yi  bacewa yake wani lokaci don haka tun da na riga na dauki kayana  watsi nike da resit, amma risit na Nita ina adana shi don kiyaye wata matsala kowani rikici.”

Resit  na da muhimmanci sosai

Adana resit na siyayya yana da muhimmanci domin kare haƙƙoƙi da kuma tabbatar da hada-hadar kuɗi tsakanin mai saye da mai siyarwa. Malam Lawali Issa, masanin tattalin arziki y ace “resit takarda ce mai matukar muhimmanci ta shaidar anyi hada hadar kasuwanci tsakanin mai saye da siyawar, kuma hujja ce ta an biya kudi sun shiga asusun ka , abu na biyu risit na da muhimmanci wajen saukake wa yan kasuwa da kamfanoni yin raskuna shigar kudi da fitarsu da kuma yin kididiga lokaci zuwa lokaci, sannan risit hujja ce dake tabbatar da biyan haraji ga gwamnati.”

“Domin samun a mayar ma ka da kuɗinka ko sauya maka  kayanka da kuma guje wa rigima  ko rishin jituwa tsakanin mai saye da mai siyarwa dole ne ka adana risit din siyayya na aƙalla shekaru 10” a  cewar Lawali Issa.

Masanin tattalin arzikin ya kara da cewa“Idan wata rigima ta taso tsakanin mai saye da mai siyarwa to risit ne ke warwareta, baya  ga haka risit na sa yarda tsakanin dan kasuwa da abokanin huldarsa sannan ingantacen  risit na dauke da lamba da ranar aka yi hada hadar da kayanda aka siya da kuma tambarin dan kasuwar da sa hanunsa, a dokance ana aje risit a kalla shekaru 10”

Duk mai sayen kaya  baya adana risit  yana fuskantar haɗarin asarar kuɗinsa ko kayansa don haka idan har kana son kiyaye asara to ka adana risit na siyayya.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )