Zazzabin cizon sabro cutar da tafi barazana ga al’ummar Maradi

Zazzabin cizon sabro cutar da tafi barazana ga al’ummar Maradi

Kare kai daga zazzabin cizon sabro ba a cibiyoyin lafiya kawai yake farawa ba, yana farawa ne daga cikin gida. Yayin da lokacin Damina ke ƙara haɗarin lamuwa da cutar sosai.Zazzabin cizon sabro ya daɗe yana zama babbar barazana ga al'ummar birnin Maradi. Duk da bincike iri-iri da ake yi, har yanzu ba a sami maganin da zai murƙushe cutar baki ɗaya ba. Domin haka, kare kai shi ne babbar makamin yaƙi da wannan annoba.

Amfani da gidan sabro mai magani na zama babban rigakafin zazzabin cizon sabro

Zazzabin cizon sabro cutar da tafi barazana ga al’ummar Maradi

Kare kai daga zazzabin cizon sabro ba a cibiyoyin lafiya kawai yake farawa ba, yana farawa ne daga cikin gida. Yayin da lokacin Damina ke ƙara haɗarin lamuwa da cutar sosai.Zazzabin cizon sabro ya daɗe yana zama babbar barazana ga al’ummar birnin Maradi. Duk da bincike iri-iri da ake yi, har yanzu ba a sami maganin da zai murƙushe cutar baki ɗaya ba. Domin haka, kare kai shi ne babbar makamin yaƙi da wannan annoba.

‎Mariama Abdoulaye wata uwa ce, da bayanan hanyoyin da take amfani da su domin kare iyalinta daga zazzabin cizon sabro.

‎”A yanzu Damina lokacin  sabro ne,kuma duk wanda yace sabro yace massasara .mu dai, akwai abubuwa kala kala,in marice ya yi abin da muke yi,  akwai wani turaren  jiji da muke sawa a dakunanmu daga 6 na yamma zuwa 9 na dare,yana sa  sauron duka ya fita,.sannan a kulla sange a saka  yara, tare da hanasu fita,idan kallon tele ne ma bai hana yaro daga cikin sange yayi kallonsa,  ba ma sakin yara a haka nan.”

‎Amfani da gidan sabro mai magani na zama babban rigakafin zazzabin cizon sabro

A nasa bangare  Zaneidu Abubakar wani magidanci na mai ra’ayin cewa «  amfani da gidan sauro mai magani da wasu magungunan gargajiya su ne muhimman hanyoyin kariya. Sakaci kaɗan na iya jawo kamuwa da cutar. Mu dai muna iya kokarin mu,wani bi sange dai muke sanya wa da yara amma wani bi kasan yaro,koda ka sanya shi sange kafin ya kwanta,wannan dan motsin da yake kafin barcin shi kaga sauro yayi mishi aiki.Wani bi kuma a sayi  mai a basu suna dan shashshafawa »

‎Zanaidu Abubakar ya kara da cewa « wani matakin indan  bamu shafa mai ba, sai mu sanya safar kafa ko riga mai dogon hannu. mutun indai ya yi  sakaci zai dinga safa da Marwa wajan da likitoci, alhali yanzu babu kudade a hannun jama’a don haka rigakafi yafi magani, musaman idan aka ce yaro bai da jini ko sai anyi karin ruwa duk wannan matsala ce »

‎Ga iyalai na birnin Maradi, kasancewa cikin sa ido a kowace faɗuwar rana shi ne tsari, domin a kan zazzabin cizon sabro, rigakafi na yau da kullum shi ne mafi kyawon kariya.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )