
Muhimmancin ban nono tsantsa ga yaro
ko a bangaren fahimtar karatu, yaron da akayi wa ban nono yafi fahimta cikin sauri akan wanda ba’ayi ma ba.
Ban nono tsantsa yana nufin shakuwa, karfi da ma wata rayuwa mai muhimmanci musamman gawanda aka yi washi. Tsarin kan sa, ba wai yana nufin shayar da yaro bane, a’a har ma yana bada lafiya ga yaro mai cike da kuzari.
Ban nono tsantsa na nufin shayar da yaro tsantsar nono tun daga ranar haihuwar sa harzuwa watanni shidda ba tare da an bashi ruwa ko abinci ba. Mme Rayyana Amadu mai kula da cimakar Dan Adam da kuma yaki da cutar tamowa ta bayyana mana muhimmancin ban nono tsantsa ga yaro. Ta na mai cewa
« shi ban nono tsantsa yana da amfani sosai ga yaro, wajen uwa da ma wajen uba kai har ma wajen al’umma baki daya. Abinda ya sa ban nono tsantsa yake da muhimmanci shine, wajen kaso 90% na nono duk ruwa ne. Dan haka yana yi wa yaro garkuwa kwarai kan cututtuka. Kuma yaron da aka yi wa ban nono tsantsa bai cika yin rashin lafiya ba kuma ko yayi bai galabaita kamar wanda ba a yima ban nono tsantsa ba, Sannan ko a bangaren fahimtar karatu, yaron da akayi wa ban nono yafi fahimta cikin sauri akan wanda ba’ayi ma ba. »
Taka rawar iyaye maza wajen taimakawa matansu gudanar da ban nono tsantsa.
Rabilou Musa, wani uba ne dake nan Maradi daya bayar da goyon baya aka gudanar da ban nono tsantsa ga yar’sa ta farko ya bayyana sauyin da ya gani bayan an yi mata ban nono tsantsa.
« Abu na farko shine zaku lura da cewa akwai sauki wajen yawan kamuwa da cututtuka ga yaron da ake yi wa ban nono tsantsa. Na biyu akwai sauki kan cututtakan dake da alaka da fitar hakori matauna da suke sa yaro ya rame har ta kai shi ga kamuwa da tamowa irin su zawo, masassara ko amai. A takaice ba zaka san lokacin da hakorinsa zasu fita ba har sai ka zo wasa da shi zaka lura da hakan. Abu na uku shine shakuwa tsakanin da da mahaifiyarsa. Zai shaku da ita sosai. »
A daya bangaren Rabilu Musa ya ja hankalin maza wajen tallafawa matansu don gudanar da ban nono tsantsa gayarensu saboda muhimmancinsa.
« Anan ina jan hankalin iyaye maza wajen bayar da goyon baya don gudanar da ban nono tsantsa gayaransu ta hanyar sayawa uwa abincin da zai gina jikinta lura da cewa irin abinci da uwa ta ci, shine yaro zai ci. »
Gudanar da ban nono tsantsa daga ranar haihuwa zuwawatanni shidda ga yaro kamar tsara cikkakar lafiya mai inganci ce ga manyan gobe. Dan haka zabin mai sauki ne, muhimmancin ban nono tsantsa tabbas na da alaka da ingantatta rayuwa ne.

