Sadaka da taimakon juna: Me ya sa wasu ke ganin an fara samun koma baya?

Sadaka da taimakon juna: Me ya sa wasu ke ganin an fara samun koma baya?

«Har yanzu akwai mutane da yawa da ba sa iya haɗa abin da zai ishe su. Su ne ya kamata a fi mayar da hankali wajen taimaka musu .» 

Ba wa mai buƙata, raba abin da mutum yake da shi da maƙwabcinsa ko taimaka wa wanda yake cikin hali na ƙunci, abubuwa ne da suka daɗe suna daga cikin muhimman dabi’un zamantakewa. Sai dai a yau, wasu daga cikin al’umma na ganin cewa sadaka da taimakon juna suna ƙara raguwa.

Matsin tattalin arziki, rashin yarda tsakanin mutane da sauye-sauyen halaye na daga cikin dalilan da ake danganta wannan koma baya da su. Amma a wajen wasu malamai da masu ruwa da tsaki a harkokin zamantakewa, sadaka da taimakon juna na ci gaba da kasancewa wata hanya mai muhimmanci ta rage talauci da ƙarfafa haɗin kai.

Sadaka ta ragu sosai a ‘yan shekarun nan

A cewar Moussa, abin da yake gani a bayyane yake. Ya ce a shekarun baya, masu hali sun fi taimaka wa marasa galihu fiye da yadda ake gani a yau.

A cewarsa, ɗaya daga cikin abubuwan da suka haifar da wannan yanayi shi ne ƙarancin yarda tsakanin mutane.

«Sadaka ta ragu sosai a ‘yan kwanakin nan. Idan aka kwatanta da shekarun baya, masu hali suna taimaka wa marasa galihu sosai. Kana iya taimaka wa mutum da jari domin ya fara sana’a, amma daga ƙarshe abin zai iya zama matsala tsakaninku» in ji Moussa cikin damuwa.

Sai dai ya ce duk da cewa wasu matasa suna ƙoƙarin dogaro da kansu, har yanzu akwai mutane da dama a cikin unguwanni da ke fama da matsanancin hali.

«Har yanzu akwai mutane da yawa da ba sa iya haɗa abin da zai ishe su. Su ne ya kamata a fi mayar da hankali wajen taimaka musu .»  ya jaddada.

Sadaka hanya ce ta rage talauci 

A nasa ɓangaren, malamin addini Sheikh Abou Saley, ya bayyana cewa sadaka ba kawai taimako ne na mutum ga mutum ba, illa wata muhimmiyar hanya ce da za ta iya taimakawa wajen gina al’umma mai adalci.

«Idan aka aiwatar da ita yadda ya kamata a cikin al’ummar Musulmi, sadaka na taimakawa wajen rage talauci » in ji malamin.

Ya bayyana cewa sadaka na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci, ’yan’uwantaka da haɗin kai tsakanin al’umma, tare da bai wa marasa galihu damar samun abin da zai taimaka musu wajen biyan bukatunsu.

Sheikh Abou Saley ya kuma yi nuni da irin muhimmiyar rawar da sadaka ke takawa ta fuskar tattalin arziki.

«Tana bai wa talaka damar samun abin da zai taimaka masa wajen biyan bukatunsa. Hakan na iya bunƙasa kasuwanci, ƙara samar da dukiya tare da rage talauci »  in ji shi.

Malamin ya kuma yi kira da a sake duba yadda ake tsara wasu hanyoyin taimakon juna da Musulunci ya tanada, musamman batun zakka. A cewarsa, idan aka tsara tattarawa da rabon zakka yadda ya kamata, za a iya samar da wata muhimmiyar hanya ta taimaka wa marasa galihu.

« Wajibi ne ƙasashenmu na Musulmi su sake duba yadda muke gudanar da rayuwarmu, musamman a ɓangaren sadaka da zakka » a cewar sa.

A cikin al’ummar da ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa, sadaka da taimakon juna na ci gaba da kasancewa muhimman hanyoyi na ƙarfafa zumunci tsakanin mutane. Duk da sauye-sauyen da ake samu a hanyoyin taimako, Moussa da Sheikh Abou Saley sun yi ittifaki kan muhimmancin taimaka wa masu rauni da marasa galihu, gwargwadon ƙarfin kowa.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )