
Tsufa cikin koshin lafiya: Hanyoyi masu sauƙi na ci gaba da kasancewa cikin ƙoshin lafiya.
« Ina yin ayyukan gida cikin hankali. Ba na debo ruwa, ba na ɗaukar kaya masu nauyi, kuma na rage daka saboda ba ni da ƙarfin da nake da shi a baya. Amma ina ci gaba da yin wasu ayyuka domin kada in zauna babu abin yi kuma jikina ya yi rauni. »
Tsufa ba yana nufin rasa lafiya ko daina gudanar da rayuwa yadda ya kamata ba. Cin abinci mai kyau, motsa jiki akai-akai, kyakkyawar hulɗa da jama’a da kuma kiyaye muhalli daga haɗarin faɗuwa na daga cikin abubuwan da za su taimaka wa tsofaffi su ci gaba da rayuwa cikin koshin lafiya. A Maradi, wasu tsofaffi sun bayyana yadda suke kula da lafiyarsu a kullum.
Yayin da yawan tsofaffi ke ƙaruwa, kula da lafiyarsu na zama wani muhimmin al’amari a cikin al’umma. Amma mene ne ya kamata mutum ya yi domin ya tsufa cikin koshin lafiya tare da ci gaba da kasancewa mai ƙarfi ?
Cin abinci mai kyau, ginshiƙin lafiya
Abu na farko shi ne abinci. Cin abinci iri-iri mai ɗauke da sinadarai masu amfani ga jiki na taimakawa sosai wajen kiyaye lafiyar tsofaffi.
Malam Rabiou mai shekaru 65 ya ce ya sauya yadda yake cin abinci domin kula da lafiyarsa.
« Ina mai da hankali sosai kan abin da nake ci. Na daina amfani da kayan ƙara ɗanɗano a abinci. Domin idan na ci shi, ina jin gajiya tare da ciwon gaɓoɓi. Matana ma sun sani, har a abincin gida ba sa amfani da shi. Ina yawan cin kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa. Tun daga lemu har zuwa kankana, ina saya domin iyali su ci. Ina matuƙar son su. Haka kuma, ina rage cin abinci mai yawan mai ko sukari. Tun lokacin da na fara wannan tsarin, ina jin jikina ya fi kyau sosai. » inji shi.
Motsa jiki domin ci gaba da kasancewa cikin ƙarfi
Motsa jiki ma yana daga cikin muhimman hanyoyin kula da lafiya yayin tsufa. Yin tafiya, motsa jiki cikin sauƙi ko wasu ayyukan da suka dace da ƙarfin mutum na taimakawa wajen ci gaba da motsin jiki.
Alhaji Garba kuwa ya zaɓi keke a matsayin hanyar sufuri da kuma motsa jiki a kullum.
« Idan na hau keke, kamar ina yin motsa jiki ne. Ina da wata matsala a ƙafafuna, saboda haka nakan yi amfani da keke wajen zirga-zirga domin guje wa wasu matsaloli. Ina jin jikina lafiya sosai. Ko da shekaruna sun ja, hawa keke yana taimaka min in kasance cikin ƙarfi a kowace rana. » a cewar shi.
A cewarsa, motsa jiki ba lallai sai mutum ya je wurin motsa jiki ba. Abu mafi muhimmanci shi ne mutum ya ci gaba da motsa jikinsa gwargwadon ƙarfinsa.
Yin ayyuka cikin hankali ba tare da cutar da kai ba
Ramatou mai shekaru 66, wadda ke aikin share-share da kula da gida, ita ma tana yin ayyukan gida amma cikin tsari da taka-tsantsan. Ba ta son zama babu abin yi, amma kuma tana guje wa ayyukan da suka fi ƙarfin jikinta saboda tsoron samun rauni.
« Ina yin ayyukan gida cikin hankali. Ba na debo ruwa, ba na ɗaukar kaya masu nauyi, kuma na rage daka saboda ba ni da ƙarfin da nake da shi a baya. Amma ina ci gaba da yin wasu ayyuka domin kada in zauna babu abin yi kuma jikina ya yi rauni. » ta fayace muna.
Misalinta na nuna cewa tsofaffi na iya ci gaba da kasancewa masu motsa jiki, amma dole ne ayyukan su dace da ƙarfin jikinsu.
Me masana lafiya ke cewa ?
Docta Fataou Chaibou, likita a Hopital de Reference ta Maradi, ya bayyana cewa tsofaffi suna bukatar kulawa ta musamman, musamman ta fuskar abinci, motsa jiki da kuma duba lafiyarsu akai-akai.
Haka kuma, masanin ya ba da shawarar ci gaba da hulɗa da jama’a domin guje wa kaɗaici, tare da tabbatar da cewa muhalli yana da aminci domin rage haɗarin faɗuwa.
Duba lafiya a kai a kai ma na da matuƙar muhimmanci, domin yayin da shekaru ke ƙaruwa, jiki kan fi fuskantar wasu cututtuka.
A ƙarshe, tsufa cikin koshin lafiya yana dogara ne da wasu halaye masu sauƙi: cin abinci mai kyau, motsa jiki akai-akai, ci gaba da hulɗa da jama’a da kuma kiyaye muhalli daga haɗari.

