
SARRAFA SHARA A MATSAYIN ARZIKI: YADDA SANA’AR SAKE AMFANI DA SHARA KE TAIMAKAWA WAJEN KARE MUHALLI A MARADI
A wani yunkuri na kare muhalli da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai, wasu ‘yan kasuwa da masu sana’o’i a Kasuwar Kadiro da ke birnin Maradi sun dukufa wajen sarrafa sharar da ake zubarwa, kamar tsofaffin karafa, kwalaye, gwangwanayen lemu, roba da sauran kayayyaki, zuwa wasu sababbin kayayyakin amfanin yau da kullum.
Wannan sana’a na taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan sharar da ke gurbata muhalli, tare da samar da guraben sana’a da hanyoyin samun abin dogaro ga masu gudanar da ita.
Haruna Mai Akwati, daya daga cikin masu wannan sana’a, ya bayyana cewa tsofaffin karafunan da a baya ake daukarsu a matsayin shara sun fara karanci, sakamakon yadda ake kara bukatarsu domin sarrafawa zuwa wasu kayayyaki masu amfani.
A cewarsa, sana’ar sarrafa tsofaffin karafa na iya zama wata hanya ta samun abin dogaro ga duk wanda ya rungumeta.
Ya ce: “Kusan in ce maka yanzu babu dagolon shara ta karfe, saboda neman ta ake yi don a sarrafa ta don wasu abubuwan ci gaba, amma ba a samu. Don haka, sana’ar sarrafa tsofaffin sharar karafa idan mutane suka rungumeta, to za su samu abinci. Mu yanzu nan ka ga muna sarrafa su zuwa akwati, ko abin ban ruwa na fadama (arrosoir), ko na’urar sarrafa kayan amfanin gona da dai sauransu. Alhamdulillahi, muna yin abubuwa da dama da su.”
A daya bangaren kuma, sarrafa tsofaffin kwalaye da sauran kayan da aka zubar na daga cikin hanyoyin rage gurbacewar muhalli. Masu wannan sana’a na ganin cewa abubuwan da mutane ke kallon shara na iya zama masu amfani idan aka sarrafasu yadda ya kamata.
Usman Ibrahim, wanda aka fi sani da Bin Affan, kwararre ne wajen sarrafa tsofaffin kwalaye da sauran kayayyakin da aka zubar zuwa kayan ado da na amfani a gida. Ya bayyana cewa kusan duk wani abu da ake zubarwa na iya samun wata sabuwar rayuwa ta hanyar kirkire-kirkire.
Ya ce: “Abubuwan da kake tunani na shara da ake zubarwa, to gaskiya ba shara ba ce. Mu ne muke kallonsu a matsayin haka. Amma idan ka yi nazari, duk abin da za ka dauka ka yi aiki da shi, to a karshe akwai wani amfani da za a yi da shi. Ni ina aiki da su, amma na fi kirkirar wasu abubuwa da su.
“Duk abubuwan da nake yi da kwali ne nake yinsu da aka zubar cikin shara. Gaskiya ina sarrafa kwalin, ko leda, ko roba, da tuyau na karto wanda ake zubarwa idan an fitar da yadi, zuwa abubuwa da dama na aikin hannu. Ka ga wannan shara, babu abin da ba na yi da ita. Muna yin kwalliyar gidaje (decoration) da su, da abin dorawa kan tebur na falo, da kayan wasan yara, har ma da manyan hotuna (agrandir).”
Baya ga sarrafa karafa da kwalaye, ana kuma samun wata hanyar amfani da ragowar kayan amfanin gona wajen kare muhalli da samar da abincin dabbobi. Wannan hanya na taimakawa wajen rage kona ragowar amfanin gona da manoma ke yi a lokacin sassabe, wanda ke iya haddasa gurbacewar iska da sauran illolin muhalli.
A karkashin wannan tsari, ana tattara ragowar amfanin gona kamar karan hatsi, dawa da masara, sannan a sarrafa su tare da wasu sinadarai na abinci domin samar da abincin dabbobi mai saukin samu.
Abdulrazak Sanusi, wanda ke aiki a wani projet da kae kira ARIDEL, ya bayyana cewa manufarsu ita ce mayar da ragowar kayan gona zuwa abincin dabbobi, domin rage barnatar da su da kuma taimakawa makiyaya wajen samun abinci mai rahusa.
Ya ce: “Muna sarrafa kayan daudar gona ko daji wadanda suke fitowa kamar karan hatsi, ko na dawa, ko na masara. Mun lura manoma suna kona su a lokacin sassabe, wanda hakan yake haifar da illa ga muhalli. Maimakon haka ne ya sa muke kwashe wadannan kara, sai mu nike su sannan mu sarrafa su.
“Daga nan sai mu hade su da ‘ya’yan gawo, kalgo, diyan kirya, ‘ya’yan dashi da na kasari. Daga nan sai mu cakuda su tare don mu samu abin da ake kira da dusar kara, saboda mu a nan Nijar ba ma noman alkama sosai. Ita kuma dusar alkama tana yi wa makiyayanmu tsada, inda take kaiwa matakin da ba za su iya sayenta ba. To, ka ga kenan, ita wannan dusar kara idan aka yada ta sosai-sosai, kuma makiyayanmu suka gane ta, sai ka ga ta samu karbuwa a kan ta alkama.”
Duk da cewa mutane da dama na kallon sharar da ake zubarwa a matsayin abubuwan da ba su da wani amfani, ayyukan wadannan masu sana’a sun nuna cewa za a iya mayar da ita wata hanya ta samar da arziki da inganta muhalli.
Sarrafa shara da ragowar kayan amfanin gona na da fa’ida iri biyu: na farko, rage gurbacewar muhalli ta hanyar hana zubar da shara barkatai da kona ragowar amfanin gona; na biyu kuma, samar da sana’o’i da hanyoyin samun abin dogaro ga matasa da sauran al’umma.
Saboda haka, bunkasa irin wadannan sana’o’i na iya zama wata muhimmiyar hanya ta kare muhalli da ci gaban tattalin arziki, tare da karfafa tunanin cewa abin da ake kira shara a yau na iya zama arzikin gobe.

