Lafiyar kwakwalwa: Alamomin gargaɗi da bai kamata a yi watsi da su ba.

Lafiyar kwakwalwa: Alamomin gargaɗi da bai kamata a yi watsi da su ba.

“Kada a riƙa yanke wa mutum hukunci ko ɗora masa laifi. Ya kamata a saurare shi da kyau, a ba shi shawara, a nuna masa goyon baya tare da tausaya masa,”

Lafiyar kwakwalwa na ci gaba da kasancewa wani batu da mutane da dama ke jin kunyar magana a kansa, saboda shiru da kuma ra’ayoyin da ba su dace ba da ke tattare da shi. Duk da haka, wasu sauye-sauye a halayen mutum na iya nuna cewa yana fuskantar matsalar damuwa ta tunani, wadda ke buƙatar kulawa da magani.  Wa’ane alamomi ne  ga iyalai da abokan hulɗa ya kamata da su kula da alamomin gargaɗi, tare da ba wa masu fama da irin wannan matsala damar samun sauraro, goyon baya da taimako ? 

Sauye-sauyen hali da bai kamata a yi watsi da su ba : 

Lafiyar kwakwalwa ba ta nufin rashin cututtukan da suka shafi tunani kawai ba. Ta kuma shafi yadda mutum yake fuskantar matsalolin rayuwa, hulɗa da sauran mutane da kuma gudanar da ayyukansa na yau da kullum.

Duk da haka, wasu mutane kan shiga cikin damuwa ta tunani ba tare da sun iya bayyana abin da ke damunsu ba. A cewar Dokta Fataou Chaibou, na asibitin kwarari ta Maradi , sauye-sauyen da ba a saba gani ba a halayen mutum ya kamata su ja hankalin na kusa da shi.

“Idan mutum yana fuskantar matsala ta fuskar lafiyar kwakwalwa, abu mafi muhimmanci shi ne kula da sauye-sauyen da ba a saba gani ba. ware kai daga jama’a, yawan baƙin ciki da ba ya gushewa, rashin sha’awar abubuwan da mutum ya saba jin daɗinsu da kuma rashin kuzarin yin ayyuka na iya zama alamomin gargaɗi.” in ji shi.

Haka kuma, yawan damuwa da fargaba fiye da kima na iya nuna cewa mutum yana fama da matsalar lafiyar kwakwalwa. Sauran alamomin sun haɗa da matsalar barci, rashin cin abinci tare da ramewa, yawan fushi ko tashin hankali, da kuma sakaci da tsaftar jiki a hankali.

Sauraro, ba da goyon baya da ƙarfafa neman likita :

Idan aka lura da waɗannan alamomi, yadda iyali da abokan hulɗa suke mu’amala da wanda abin ya shafa na da matuƙar muhimmanci. Dokta Fataou Chaibou ya jaddada cewa bai kamata a riƙa yi wa mutum hukunci ko ɗora masa laifi ba. Maimakon haka, ya kamata a saurare shi cikin natsuwa domin ya samu damar bayyana abin da yake damunsa.

“Kada a riƙa yanke wa mutum hukunci ko ɗora masa laifi. Ya kamata a saurare shi da kyau, a ba shi shawara, a nuna masa goyon baya tare da tausaya masa,” in ji shi.

Likitan ya kuma ba da shawarar ƙarfafa mutanen da suke fuskantar irin wannan matsala da su nemi taimakon ƙwararrun ma’aikatan lafiya, musamman a cibiyoyin lafiya da ke da sashen kula da lafiyar tunani ko na masu tabin hankali.

“Ya kamata a kasance tare da mutum a kowane lokaci tare da taimaka masa,” in ji Dokta Fataou Chaibou.

Don haka, ya kamata a ba lafiyar kwakwalwa muhimmanci kamar yadda ake ba lafiyar jiki. Fasa shirun da ke tattare da matsalolin lafiyar kwakwalwa, yaƙi da kyama da nuna wariya ga masu fama da su, da kuma sauƙaƙa musu samun kulawar lafiya, duk hanyoyi ne da za su taimaka wajen inganta kulawa da waɗanda ke fama da matsalar damuwa ta tunani.

 

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )