
Har yanzu ana sarrafa Burkutu giyar gargajiya a wasu yankunan Jihar Maradi
Gidan Hasiya na tara mashaya Burkutu baki dake zuwa daga kauyuka daban daban da yan gari mashaya Umaru Mati wani dattijo mai shekaru 66, tun daga garin Turumbudi yake zuwa shan Burkutu El Koshe kuma yana shan tiya uku, kudinta dala sittin.
Shekaru 19 kenan da majalisar Dinkin Duniya ke tuni da ranar shan barasa, a Jamhuriyar Nijar duk da cewa shan barasa ya ja baya a cikin birane, a karkara har yanzu wasu mutane na shan Burkutu cewa da giyar da ake sarrafawa da Hatsi. A kasuwar El koshe dake garin El kokiya cikin karamar hukumar Jiratawa, Hasiya Isufu mai shekaru 46, shekaru 15 kenan take sana’ar dafa Burkutu da take siyarwa kasuwannin Tsibiri, Bamo da kasuwa El koshe.
Kafin ta kai ga saida burkutun, Hasiya Isufu na daukar kwanaki tana sarrafa giyar. « Farkon burkutu tsaba ce ake diba a zuba cikin ruwa sai ta kwana guda sannan a tsame sai kuma a tsimata sai tayi tsiro tsawan kwanaki biyu, daga nan kuma a shanya ta, ta bushe sai a auna kwatankwacin tiya daya ta hada burkutun. » Ba nan aiki, ya tsaya ba : « sai niko garin na Hatsi, sannan a zuba garin cikin tunkunya ayita dafuwarta tsawon kwanaki uku a kashe a sabke, ta huce, atace to burkutu ta hadu Kenan ».
Har yanzu burkutu na da dumbin mashaya
Gidan Hasiya na tara mashaya Burkutu baki dake zuwa daga kauyuka daban daban da yan gari mashaya Umaru Mati wani dattijo mai shekaru 66, tun daga garin Turumbudi yake zuwa shan Burkutu El Koshe kuma yana shan tiya uku, kudinta dala sittin. « In nasha Burkutu sai inji lafiya lau ,can kuma sai inji kai na na girgizawa kuma sai muji lafiya lau cikin cikinmu tana tafiya », injin shi.
A mashayar, na taras da Salifu dan gidan Mai Agwada yana shan Burkutun Hasiya shi da tawagarsa. « Maganar giya ina shan giyar Burkutu gidan Hasia, ko gobe ina zuwa in bada kudi na ta bani tiya biyu tiya uku in sha in ba tawagata. »
Ko baya ga saida Burkutu da Hasiya keyi cikin kasuwanni masu shagalin biki a karkara na odar Burkutun Hasiya domin liskewa da yan uwansu ranar biki , sannan binciken masana ya tabbatar da Shan Barasa dai yana haddasa cututtuka daban daban ga lafiyar bil Adama to saidai ita Burkutu babu wani bincike daya tabbatar da hakan, kuma ana yin ta Hatsi ana yin ta dawa sannan tana daukar kwanaki 5 tun daga jika Hatsin da tsuma shi yayi tsiro har karasa dafuwarta.

