
Matsalar samun haihuwa: anfanin neman chawarwarin kiwon lafiya ga ma’aurata ?
«Dalilan matsalar na iya kasancewa daga mace, daga namiji, daga bangarorin biyu, ko kuma a wasu lokuta ba a gano takamaiman dalili ba »
Matsalar iya samun haihuwa na iya zama sanadin damuwa, matsin lamba daga al’umma, har ma da rashin jituwa tsakanin ma’aurata. Sai dai neman taimakon ma’aikacin lafiya da wuri na iya taimakawa wajen gano abubuwan da ka iya haifar da matsalar da kuma samun kulawar da ta dace. Moustapha Mainassara, mai gabatar da shirin lafiyar jima’i, ya yi bayani kan matakan da ma’auratan da ke fuskantar matsalar iya samun haihuwa ya kamata su ɗauka.
Yaushe ya kamata a je neman taimakon lafiya?
Idan ma’aurata suna saduwa akai-akai ba tare da amfani da hanyar hana ɗaukar ciki ba, amma ba a samu ciki ba bayan watanni 12, ana ba da shawarar su tuntubi ma’aikacin lafiya.
«Idan ma’aurata suna saduwa akai-akai ba tare da amfani da hanyar hana ɗaukar ciki ba, amma ba a samu ciki ba bayan watanni 12, ya kamata su tuntubi ma’aikacin lafiya,” in ji Moustapha Mainassara.
Ga mace mai shekaru 35 ko fiye, ana iya neman shawarar ma’aikacin lafiya bayan watanni shida na ƙoƙarin samun ciki. Haka kuma, bai kamata a jira ba idan akwai wasu matsaloli kamar rashin daidaituwar al’ada, tarihin kamuwa da cututtukan al’aura, yin tiyata ko wasu matsalolin lafiya da aka sani za su iya shafar iya samun haihuwa.
Matsalar iya samun haihuwa ta shafi ma’aurata biyu :
A cewar Moustapha Mainassara, bai kamata a ɗora alhakin matsalar iya samun haihuwa kai tsaye kan mace ba. Ya ce ya dace a duba lafiyar ma’auratan biyu domin gano abin da ka iya haifar da matsalar.
«Matsalar iya samun haihuwa ta shafi ma’aurata, kuma ya dace a duba lafiyar su biyun» in ji shi.
Matakin farko shi ne zuwa wata cibiyar lafiya, inda ma’aikacin lafiya zai saurari ma’auratan, ya binciki tarihin lafiyarsu, sannan ya ba da shawarar gwaje-gwajen da suka dace.
A bangaren mace, ana iya yin wasu gwaje-gwaje domin tantance yadda kwai ke fitowa da kuma yanayin sassan haihuwa. A bangaren namiji kuma, ana iya yin spermogram, wato gwajin maniyyin namiji.
Moustapha Mainassara ya kuma jaddada muhimmancin guje wa zargi ko ɗora laifi kan ɗaya daga cikin ma’auratan.
«Dalilan matsalar na iya kasancewa daga mace, daga namiji, daga bangarorin biyu, ko kuma a wasu lokuta ba a gano takamaiman dalili ba » ya bayyana.
A gare shi, abin da ya fi muhimmanci shi ne ma’aurata su yi magana cikin fahimta, su je neman taimakon lafiya tare, sannan su bi shawarar kwararrun ma’aikatan lafiya.
« Abu mafi muhimmanci shi ne kada a yi shiru ko zargin juna. Zuwa neman taimakon lafiya tare, gano dalilin matsalar da kuma samun kulawar da ta dace su ne matakan farko na fuskantar wannan matsala » in ji Moustapha Mainassara.

