Illar shan lemuna masu zaki fiye da mussali lokutan bukukuwa a Maradi.

Illar shan lemuna masu zaki fiye da mussali lokutan bukukuwa a Maradi.

« na sha roba guda lemun zaƙi  ni a gaskia nafison lemu orange,yau dai nasha roba guda.E munji ana cewa yana sa cututuka amma dai muna sha  ga  al'ada.»

A Maradi yayin shagulgulan aure ko suna ko wani biki, shan lemuna  masu zaƙi , da sauran abubuwan sha na masana’antu masu zaki,ya zama wani muhimmin ɓangare na bukukuwan zamantakewa kamar aure, suna da kuma bukukuwan addini. Sai dai yawan shan irin waɗannan  lemuna  sha na iya zama haɗari ga lafiyar ɗan Adam.

Wani matashi Jamilou Sa’adou,  sabon angon mai  shekara 30, ya kashe kuɗi kimanin CFA 40,000 zuwa 50,000 wajen sayen lemunan sha masu zaƙi a lokacin bikin aurensa.

 « Na sayi Maltina, gwangwani, da kuma Fanta Orange. Na sayi na kimanin jika goma  10,000. Wallahi, hakan ya faru ne saboda ya riga ya zama al’ada a gare mu. Mun saba da shi kuma muna jin dadinsa. Don haka, kowa yana sha. Wasu suna cewa yana iya kawo matsalar lafiya, amma mu kam muna sha. Ana rarraba waɗannan abubuwan sha ga kowa da kowa lokacin bukukuwa, ga mata da maza, da duk wanda Allah ya ƙaddara zai samu. Ana rarraba komai har sai abin da aka ajiye ya ƙare.» a cewar shi.

A yayin bukukuwan zamantakewa, matasa, tsofaffi da kuma mata suna yawan shan irin waɗannan abubuwan sha masu zaƙi da gas.

A cewar Chamsoudine Rabiou Issoufou, wani matashi daya  raba lemuna zaki wajen bikin Jamilou Sa’adou,« na sha roba guda lemun zaƙi  ni a gaskia nafison lemu orange,yau dai nasha roba guda.E munji ana cewa yana sa cututuka amma dai muna sha  ga  al’ada.»

Masana kamar Dokta Seidy Cheik, ƙwararren  likitan  a fannin rigakafin cututtuka, yawan shan abubuwan sha masu zaƙi na iya haifar da cututtuka daban-daban.

« Yau a’umma da dama na shan lemunan zaki hiye da musali musaman lokacin shagulgula abinda ke haddasa illoli da dama, a gaskia akwai sunadarai masu cutarwa cikin kayan da ake hada irin wadanan lemunan masu zaki,shan su na yawaita sukari cikin jini ,da tsawan lokaci ya haddasa cutar sugar,da haifar da kiba, dada nan sai kitse ya mamaye hanji sai matsala ta afku.ko baya ga haka yawan shan lemu konko mai zaki na haifar da kiba sosai,ciwon zuciya karamcin kanwa cikin jiki,daga nan kasusuwa suyi rauni sai karewar su.»inji shi.

Domin ƙara kare lafiyar jama’a, ya fi dacewa a fifita ruwan ’ya’yan itatuwa da na gargajiya, kamar bissap, tsamiya  ko lemun citta, maimakon lemunan sha masu zaƙi masu gas na masana’antu da ake sayarwa cikin gwangwani ko kwalaben roba, musamman a lokacin bukukuwan addini da manyan taruka.

Ahadi Moussa.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )