Daidaita aiki da shayarwa: ƙalubalen da mata masu aiki ke fuskanta a kullum.

Daidaita aiki da shayarwa: ƙalubalen da mata masu aiki ke fuskanta a kullum.

« Da safe kafin na shiga aji da ƙarfe takwas, nakan shayar da 'yata sannan in bar ta a hannun mai kula da ita. Da ƙarfe goma, lokacin hutu, ana kawo mini ita domin in ba ta nono kafin in koma aji. »

Haɗa aiki da shayar da jarirai na daga cikin manyan ƙalubalen da mata masu aiki ke fuskanta a yau. Tsakanin koyarwa a makaranta, ayyukan gida da kuma kula da jarirai, wasu iyaye mata suna ƙoƙarin ci gaba da shayar da ‘ya’yansu nono kaɗai kamar yadda masana lafiya suka ba da shawara.

Bayan ‘yan makonni kaɗan da haihuwa, mata da dama suna komawa bakin aiki tare da ci gaba da shayar da jariransu. Wannan yanayi na buƙatar tsari da jajircewa a kullum. Boubacar Fatsima, malamar makaranta, na daga cikin matan da suka zaɓi ci gaba da shayar da jariransu nono kaɗai duk da nauyin aiki. Tana mai cewa : « Da safe kafin na shiga aji da ƙarfe takwas, nakan shayar da ‘yata sannan in bar ta a hannun mai kula da ita. Da ƙarfe goma, lokacin hutu, ana kawo mini ita domin in ba ta nono kafin in koma aji. »

Malamar ta kuma bayyana cewa tana amfani da lokacin hutun rana domin kula da jaririnta kafin ta ci gaba da aikinta da rana.

Bambancin ƙalubale bisa ga irin aikin da mace ke yi.

Sai dai ba kowace mace ce take samun irin wannan damar ba. Wasu mata masu aikin gida ko na hannu suna fuskantar ƙarin ƙalubale wajen haɗa aiki da shayarwa. Ramatou Issaka, yer chekara 40, wadda ke aikin girki da kula da gida a wani gida, ta bayyana cewa duk lokacin da jaririyarta take buƙatar nono, tana ba ta duk da yawan ayyukan da take yi.

« Bayan ta kai wata shida, nakan bar ta a gida amma in tabbatar an shirya mata kunun gina jiki. Kamin ta Kai wata shida, in na tafi wajen aikatau, Idan ta yi kuka, nakan ba ta nono sannan in ci gaba da ayyukan gida », in ji ta.

Duk da ƙalubalen da suke fuskanta, waɗannan mata suna ƙoƙarin bin shawarwarin masana lafiya da ke ba da shawarar shayar da jarirai nono kaɗai har tsawon watanni shida na farko. Wannan na nuna irin jajircewa da sadaukarwar da iyaye mata ke yi domin tabbatar da lafiyar ‘ya’yansu.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )